Dokar Ta Baci: Sojoji Sun Mamaye Gidan Gwamnatin Ribas, An Nemi Fubara An Rasa
- An nemi Gwamna Siminalayi Fubara, an rasa shi yayin da sojoji suka mamaye gidan gwamnatin Rivers, bayan ayyana dokar ta-baci
- Hare-haren ‘yan bindiga kan bututun mai sun haddasa tashin hankali, inda gwamnatin tarayya ta dakatar da gwamnan na watanni shida
- Sojoji sun karfafa tsaro a Fatakwal, inda aka ga motocin yaki da jami’an tsaro dauke da makamai suna sintiri a gidan gwamnatin jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Rivers – An nemi gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara, an rasa a daren Talata, yayin da sojoji suka dauki matakai na tsaro a ciki da wajen da gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal.
Shigar motocin sojoji gidan gwamnatin Rivers, na zuwa ne 'yan awanni bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar.

Asali: UGC
Shugaban kasa ya dauki wannan matakin ne bayan fashewar bam a kan bututun mai na Trans-Niger Pipeline (TNP), da kuma barazanar 'yan bindiga, inji rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin 'yan bindiga kan bututun mai
Rikicin siyasa a jihar Rivers ya dauki mummunan salo bayan da wasu kungiyoyin 'yan bindiga suka yi barazanar tarwatsa bututun mai idan majalisar jihar ta ci gaba da yunkurin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.
Cikin ‘yan sa’o’i bayan da 'yan majalisa suka mika takardar zargin aikata ba daidai ba ga gwamnan, ‘yan bindigar suka aiwatar da barazanar su.
Hare-haren da aka kai kan babban bututun mai sun janyo fargaba game da tsaron yankin da kuma tasirin tattalin arziki ga wannan matakin.
Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Rivers
A matsayin martani ga tabarbarewar tsaro, Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da kuma dukkan mambobin majalisar Rivers har na tsawon watanni shida.
A cikin matakan dokar ta baci, Tinubu ya naɗa Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin 'shugaban rikon kwarya', wanda zai jagoranci jihar.
Bayan sanarwar, sojoji sun kara karfi a cikin birnin Fatakwal, inda aka ga manyan jami’an tsaro dauke da makamai suna tsaron wurare masu muhimmanci.
Shaidu sun ruwaito cewa motocin soja guda 10 ne ke yin sintiri a kusa da gidan gwamnatin jihar Rivers, yayin da aka ajiye manyan motocin yaki a wuraren tsaro masu mahimmanci.
Yanayin tashin hankali a birnin Fatakwal
Ganau sun bayyana cewa yanzu haka birnin Fatakwal na cikin firgici da fargaba, musamman a yankunan Isaac Boro Park – UTC Junction – gidan gwamnati.
Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa jaridar cewa:
"Babu kowa a kan hanyar da ta taso daga Isaac Boro Park zuwa UTC Junction da gidan gwamnati. Mutane na kokarin komawa gida don gujewa fadawa cikin rikici.
"Na hango motocin soja guda 10 suna shawagi a hanyar zuwa fadar gwamnatin jihar Rivers. Haka nan, an ajiye manyan motocin yaki a kofar shiga gidan gwamnatin."
Wasu majiyoyin tsaro sun bayyana cewa shigar dakarun soja na nufin hana duk wani yunƙurin mayar da martani ko ƙoƙarin kawo cikas bayan dakatar da Fubara.
An nemi Fubara an rasa bayan dakatar da shi
Har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto, babu tabbas ko Gwamna Fubara ya bar fadar gwamnati ko kuwa yana ciki har yanzu.
Wasu majiyoyi daga gidan gwamnati sun bayyana cewa gwamnan ya dade da hasasho yiwuwar ayyana dokar ta bacin, don haka ya shafe lokaci mai tsawo yana taruka a ranar Talata.
Wata majiya daga gidan gwamnati ta bayyana cewa Fubara da makusantansa sun yi taro na sa’o’i da dama, mai yiwuwa don tsara matakin da za su dauka bayan sanarwar Tinubu.
Wani tsohon kwamishina, wanda ya kira wakilin jaridar a waya, ya tabbatar da cewa yana cikin taron da gwamnan ya kira, amma ya ki bayar da karin bayani.
Sai dai ya yi alkawarin zai sake kira daga baya, amma bai yi hakan ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.
Asali: Legit.ng