Wani Kirista a Plateau ya gina Masallacin Juma’a domin Musulmi, yana mai cewa aikin zai ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da jituwa tsakanin al’ummar yankin.
Wani Kirista a Plateau ya gina Masallacin Juma’a domin Musulmi, yana mai cewa aikin zai ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da jituwa tsakanin al’ummar yankin.
Dan wasan barkwanci AY Makun ya ce ya daina zuwa coci saboda rade-radin da ake yi kansa, yana mai tambayar ko coci ta daina zama mafakar masu neman gafara.
Wani dan Najeriya ya baiwa matarsa kyautar sabuwar mota domin nuna soyayya da kuma godiyarsa saboda ta haifi ɗa namiji a haihuwarta ta farko a gidansa.
Oba Abdurrashid Akanbi na Iwo dake jihar Ogun ya ce bai yi nadamar karya gunki mai shekaru 800 a fadarsa ba kuma zai cigaba da riko da addinin Musulunci a rayuwarsa.
Yayin da matasa masu cin gajiyar N-power ke bin basukan watanni takwas, da alamu za su sha jar miya bayan Bola Tinubu ya juyo ta kansu kan basukan.
Duk da Hadiza Shehu Galadanci ta zama Farfesa, ba ta manta da kula da iyalinta ba. Farfesar ta ce idan ta dawo daga asibiti, abin da yake gabanta shi ne tarbiyya.
Shehin malamin Musulunci, Alkali Abubakar Zariya ya ce maganar ƙara aure da zai yi na nan daram dam. Malamin ya ce kaunar Jamila ba zai hana auren Sumayya ba.
Tsohon ministan Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu wanda ya rasu yana da shekaru 110 a duniya.
Sakamakon yajin aikin da 'yan kwadago suka yi, fitaccen mawakin Najeriya, Falz, ya ce ya yi asarar kudi mai yawa saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo.
A nan mun kawo maku alaka, dangantaka, rauwa da salsala, labari da sauran bayanai a kan ‘yar Sakin Kano, Zainab Ado Bayero da ta fito daga kudu maso kudun Najeriya.
Wani faifan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya dauki hankalin jama'a yayin da aka ga wata mata ta haifi 'yan hudu bayan shafe shekaru 18 ta na jira.
Mutane
Samu kari