Kawun Tsohon Ministan Najeriya, Farfesa Isa Pantami Ya Rasu Yana da Shekara 110

Kawun Tsohon Ministan Najeriya, Farfesa Isa Pantami Ya Rasu Yana da Shekara 110

  • Fitaccen malamin addinin musulunci, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin mutuwar yayan mahaifiyarsa, Malam Abubakar Audu
  • Tsohon ministan Najeriyan ya ce kawun nasa wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu yana da shekaru 110 a duniya
  • A yayin da ya ke jimamin mutuwar kawun na sa, Farfesa Isa Pantami ya yi addu'a ga iyaye da malaman da suka riga mu gidan gaskiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon ministan Najeriya kan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa.

Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa
Allah ya yi wa kawun Pantami rasuwa a jihar Yobe. Hoto: @ProfIsaPantami
Asali: Twitter

Farfesa Isa Pantami wanda ya yi minista a zamanin mulkin Buhari ya ce kawun nasa, Malam Abubakar Audu ya rasu yana da shekaru masu yawa a duniya.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Kawun Farfesa Pantami ya rasu a Yobe

Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a yammacin yau Talata, Pantami ya ce Malam Abubakar ya rasu a garin Hausari, karamar hukumar Machina da ke jihar Yobe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar sanarwar tsohon ministan:

"A yau kawun mu, yayan mahaifiyar mu, wato Malam Abubakar Audu wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu.
"Allah ya dauki rayuwarsa a karamar hukumar Machina a garin Hausari da ke jihar Yobe a wurin da yake rayuwa."

Farfesa Pantami ya yi wa mamacin addu'a

Sanarwar Farfesa Pantami ta ƙara da cewa Malam Dankule ya koma ga Allah ya na da sama da shekara 110 a duniya bisa kiyastawar alƙaluma.

"Allah ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa sa sauran iyayen mu da malaman mu da zuriyar mu."

In ji Farfesa Pantami.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Kungiya ta faɗi dalilin tuɓe Aminu Ado da mayar da Sanusi II da Abba ya yi

Mutane sun yi wa Pantami ta'aziyya

Ma'abota shafin X sun yi tururuwa wajen yi wa Pantami ta'aziyyar wannan rashi da ya yi.

@UmmUSerLMer:

"Allah ya gafarta mai."

@AjeeyaIk:

"InnalilLahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya kai haske kabarinsa. Makocinmu ne."

@jdeshikat:

"Allah ya gafarta masa. Allah ya kuma ya ba wa iyalai da abokanai hakurin rashin sa.

@Madawaki_Jr:

"Allah ya gafarta ma shi ya sa ya huta da duk sauran al’umar musulmi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel