Babban Mai Goyon Bayan Isra'ila Ya Mutu a Amurka bayan Ya Yabi Trump kan Iran
- Babban mai rajin kare Yahudawa a kasar Amurka, Abraham Foxman ya riga mu gidan gaskiya bayan shafe sama da shekara 80 a duniya
- Abraham Foxman ya kasance daya daga cikin makusantan shugabannin Amurka da ya ke kare hare-haren Isra'ila a Gaza da sauran yankuna
- 'Yan makonni kafin mutuwar shi, Foxman ya yaba wa shugaba Donald Trump kan kaddamar da hare-hare a kasar Iran, har ya ce hakan ya dace
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Fitaccen jagoran Yahudawa a Amurka kuma mai goyon bayan Isra’ila, Abraham Foxman wanda aka fi sani da Abe Foxman, ya rasu yana da shekara 86.
Foxman ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara yadda ake tattauna batun Isra’ila da ƙin yahudawa a Amurka tsawon shekaru masu yawa.

Kara karanta wannan
TUC ta kawowa Tinubu hanyar karya farashin fetur ta hanyar alaka da matatar Dangote

Source: Getty Images
An sanar da rasuwar Abraham Foxman
CNN ta wallafa cewa kungiyar ADL da ya jagoranta na tsawon shekara 28 ta tabbatar da rasuwarsa ranar Lahadi, inda ta bayyana shi a matsayin mai kishin Yahudawa da Isra’ila.
Shugabar kwamitin gudanarwar ADL, Nicole Munchnik ta ce Foxman ya taimaka wajen gina dimokuraɗiyya mai sassaucin ra’ayi a Amurka, inda ta bayyana shi a matsayin
“Mai ba shugabannin Amurka da na duniya shawara na tsawon lokaci.”
“Ga waɗanda suka san shi, Abe mutum ne mai karamci, aboki na kwarai, mai ba da shawara, mai son muhawara da kuma mai son runguman juna,”
In ji Munchnik.
Aikin da Foxman ya yi a ADL
An bayyana cewa Foxman ya shiga ADL ne a shekarar 1965, sannan ya zama shugaban ƙungiyar daga shekarar 1987 zuwa 2015.
A ƙarƙashin jagorancinsa, ƙungiyar – wadda ke bayyana kanta a matsayin mai sa ido kan ƙiyayya – ta zama ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin fafutuka masu tasiri a ƙasar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin tarayya ta gano kuskure, ta yi gyara a sunan da ake kiran Shugaba Bola Tinubu
Masu fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawa dai sun daɗe suna sukar ADL, suna zarginta da ɓata sunan masu goyon bayan Falasɗinu.
Tun bayan fara yaƙin Gaza na baya bayan nan, ADL ƙarƙashin magajin Foxman, Jonathan Greenblatt ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da masu sukar Isra’ila.
Matsayar Foxman kan Gaza/Iran
Foxman shi ma ya ci gaba da kasancewa mai tsayin daka wajen goyon bayan Isra’ila tare da kare matakan da take ɗauka a yaƙin Gaza.
Game da kisan kiyashin Isra'ila a Gaza, Foxman ya ce:
“Abin da ke faruwa a Gaza abin takaici ne. Amma ba kisan kiyashi ba ne. Kuma ba haramtacce ba ne,”
Makonni kaɗan kafin rasuwarsa, Foxman ya goyi bayan yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran, inda ya nuna godiya ga shugaban Amurka, Donald Trump da firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu bisa kai hari kan ƙasar.
Al Jazeera ta rahoto ya ce:
“Na gode shugaba Trump da Firaminista Netanyahu saboda yaki da tsattsauran ra’ayi. Muna fatan duniya za ta zama wuri mafi kyau da aminci a nan gaba,”

Kara karanta wannan
Dan majalisar Amurka ya harzuka kan harin Plateau, ya gayawa Trump matakin dauka kan Najeriya

Source: Getty Images
Isra'ila za ta rabu da Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan shirinsa na daina dogaro da tallafi daga Amurka.
A wata hira da aka yi da shi, Netanyahu ya sanar da cewa nan da shekara 10 masu zuwa yana so su daina karbar tallafin soji daga wata kasa.
Amurka tana mika tallafin biliyoyin daloli domin tallafawa sojojin Isra'ila duk da hare-haren da Netanyahu ke kai wa a Gaza da sauran yankuna.
Asali: Legit.ng