Sarkin Gida: 'Dan Najeriya Ya Gwangwaje Matarsa da Sabuwar Mota Bayan Ta Haifi Namiji

Sarkin Gida: 'Dan Najeriya Ya Gwangwaje Matarsa da Sabuwar Mota Bayan Ta Haifi Namiji

  • Wani dan Najeriya da ya ba matarsa kyautar sabuwar mota bayan ta haifi ɗansu na fari ya jawo magana a shafukan sada zumunta
  • An dauki bidiyon lokacin da magidancin ke mika makullin motar ga matarsa, abin da ya karade soshiyal midiya a cikin karamin lokaci
  • An ce wannan kyautar motar alama ce ta farin cikin da mijin yake ciki bayan matar ta haifi ɗa namiji a haihuwarta ta farko a gidansa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Wani ɗan Najeriya ya samu yabo daga 'yan soshiyal midiya bayan da aka ga bidoyonsa yana ba matarsa kyautar sabuwar mota.

Kamar yadda bidoyon ya yaɗu a shafin TikTok, an ce mijin wanda ke zaune a kasar waje ya ba matar kyautar motar ne saboda ta haifi ɗa namiji a haihuwarta ta farko a gidansa.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan sojojin Najeriya sun hallaka dan sanda

Bidiyon dankareriyar motar da miji ya mallakawa matarsa
Dan Najeriya ya baiwa matarsa kyautar sabuwar mota. @icparklins
Asali: TikTok

An gwangwaje mai jego da kyautar mota

Faifan bidiyon wanda @icparkliins ya wallafa a shafinsa na TikTok na dauke da taken "wannan tukuicin godiyata ne."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika, a jikin bidoyon an ga wani rubutu da ke cewa "Kin haifa wa ɗan Igbo ɗa namiji", wanda ake ganin ya nuna girman samun ɗa namiji a haihuwar fari ga mutanen Igbo.

Jama'a da dama sun jinjinawa magidancin bisa irin soyayya da kuma godiyar da ya nuna wa matar tasa da ta santalo masa ɗa namiji.

Kalli bidiyon a ƙasa:

Abin da ƴan soshiyal midiya ke cewa

Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin abin da mutane ke cewa kan wadanda ma'aurata.

Patsy Nkay:

"Ba fa duka mazan Igbo suke haka ba, masu niyya ne kawai ke yi."

BharbieDoll:

"Ta cancanci fiye da haka."

Kara karanta wannan

"Matata ta fara mani wani abu saboda bana gamsar da ita a gadon aure," Miji ya kai ƙara kotu

Ozi_oma01:

"Za mu bi duk addu'ar da ta yi da "Amin".

Iam_Yujinia:

"Ni ma ina da bukatar irin wannan farin cikin ya Ubangiji. Har zuwa lokacin da zan samu hakan, zan ci gaba da taya mutane murna."

KachamaTawina2:

"Wasu mazan Igbo na da kirki. Ni da na haifi Chinedu shekara 15 da suka wuce, mijina bai saya mun ko wayar hannu ba."

Magidanci ya yiwa matarsa kyautar Venza

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa wata 'yar Najeriya ta zub da hawaye domin farin ciki bayan mijinta ya ba ta kyautar tsaleliyar mota kirar Venza.

A cikin wani bidiyo da ya karade soshiyal midiya, an ga mijin ya ba matar kyautar motar a matsayin tukuicin nakuda da ta yi tare da haifa masa ɗa namiji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.