Gwamnati Ta Tsokano Fushin Dattawan Katsina da Aka Cafke Tsohon Malami
- A makon nan aka cafke Dr. Bashir Usman Kurfi kuma za a cigaba da rike shi a gidan gyara hali har makon gobe
- An kama tsohon malamin jami’ar kuma masanin tsaron ne bayan zarginsa da yin kalaman bata suna ga gwamnatin Katsina
- Wasu manya a jihar Katsina sun bayyana irin rawar da Bashir Kurfi yake takawa saboda kawai ya ga an samu tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Katsina - Wata kungiya ta dattawa da suka damu da cigaban jihar Katsina sun yi kiran gaggawa da a saki Bashir Usman Kurfi.
An kama masanin wanda ya saba yin sharhi a kan harkokin tsaro da kuma sauran al’amuran yau da kullum, yanzu yana tsare.

Source: Facebook
Kungiyar dattawan Katsina ta kare Bashir Kurfi
Daily Trust ta ce wata sanarwa da aka fitar ta hannun Dr. Hassan Garba, ta bayyana kokarin Dr. Bashir Kufi wajen samar da tsaro.
Kungiyar dattawan ta ce tsohon malamin jami’ar ya taka rawar gani wajen ganin bayan matsalar ‘yan bindiga da ta addabi Katsina.

Kara karanta wannan
'Yan Bindiga: Kungiyar duniya ta yi wuf ta yi magana da jin an cafke malami a Katsina
Kurfi ya yi kokarin zama da jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da nufin kawo karshen satar mutane da asarar ayuka.
Dr. Hassan Garba ya yi bayanin yadda wanda aka kaman ya rika fadi-tashi a zaurori dabam-dabam saboda a samu zaman lafiya.
Dattawan sun koka da cewa cigaba da garkame shi zai sace guiwar daidaiku da kungiyoyi da ke aiki da jami’an tsaro a jihar ta Katsina.
Akwai mutane dabam-dabam da kungiyoyi masu zaman kansu da ke taimaka wa jami’an tsaro da bayanai game da ‘yan bindiga.
Kiran da manyan suka yi wa Gwamnatin Katsina
Sanarwar ta bukaci Gwamnatin Katsina ta karkata akalarta wajen cafke’yan bindiga da sauran miyagun mutane masu barna.
Kamar yadda jaridar ta rahoto, saboda haka ne manyan suka yi kira a saki Bashir Kurfi ba tare da hukuma ta gindaya wani sharadi.
‘Yan kungiyar da suka fitar da wannan jawabi sun kunshi: Hon. Hamisu Gambo Dan Lawal, Ambasada Sani Bako da Abdullahi Hassan.
Sauran kuma su ne: Abubakar Ibrahim, Alhaji Suleiman Halliru sai kuma Hon. Jamil Dan Musa.

Source: Facebook
'Yan adawa sun bukaci a saki Bashir Kurfi
Ita ma jaridar Leadership ta ce kwamitin yakin neman zaben Ahmad Babba Kaita ya yi tir da kama tsohon malamin na jami’ar ABU Zaria.
A wani jawabi da aka fitar, kwamitin kamfen ya kira wannan lamari da keta alfarma da kuma toshe hakkin tofa albarkacin baki a Najeriya.
Abubakar Ahmed a madadin kungiyar adawar ya bukaci gwamnati da jami’an tsaro su bi doka maimakon a kama malamin a rufe shi.
Malam Abubakar Ahmed ya ce ko dai a saki dattijon ko kuma a gurfanar da shi a kotu, amma ba a cigaba da garkame shi haka kurum ba.
Kurfi shi ne wanda ya kafa Katsina Community Security Initiative (KCSI), kuma yana ta kokarin ganin an yaki ‘yan bindiga a jihohin Arewa.
Amnesty ta soki kama Dr. Kurfi a Katsina
Duniya ta amsa da aka kama Dr Bashir Kurfi saboda cewa gwamnatin jihar Katsina ta biyawa ‘yan bindiga kujerun hajji kamar yadda aka ji rahoto.
Kungiyar Amnesty International Nigeria ta yi tir da kama tsohon malamin Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma masanin tsaro saboda wasu kalamansa.
Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani yanki na murkushe 'yancin fadin albarkacin baki da tsarin mulkin kasa ya amince da shi.
Asali: Legit.ng

