Basarake Ya Fadi Dalilin Karya Gunki Mai Shekaru 800, Ya Ce Allah Ne Kaɗai Abin Bauta da Gaskiya

Basarake Ya Fadi Dalilin Karya Gunki Mai Shekaru 800, Ya Ce Allah Ne Kaɗai Abin Bauta da Gaskiya

  • Wani babban basarake a jihar Ogun, Oba Abdurrashid Akanbi ya yi magana kan karya gunki mai shekaru 800 da ke ajiye a fadarsa
  • Oba Abdurrashid Akanbi ya kuma tabbatar da cewa zai cigaba da adawa da bautar gumaka saboda ba hanyar gaskiya bace
  • Har ila yau, babban sarkin ya fadi babban dalili da yasa zai cigaba da riko da addinin Musulunci hannu biyu a rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun - Wani babban basaraken gargajiya mai rike da masarautar Iwo a jihar Ogun ya yi magana kan kakkarya gunki da ya yi a fadarsa.

Basaraken mai suna Oba Abdurrashid Akanbi ya ce ya karya gunki mai shekaru 800 ne saboda babu kyau bautar gumaka.

Kara karanta wannan

Ana cikin talauci, Tinubu ya fadi hanyar da za ta zamo mafita ga 'yan Najeriya

Oba na Iwo
Oba Abdurrashid Akanbi ya ce addinin Musulunci ne hanyar tsira. Hoto: Oba Abdurrashid Adewale Akanbi
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa zai cigaba da bautar Allah shi kadai domin ita ce hanyar tsira a duniya da lahira.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin karya gunki mai shekaru 800

Oba Abdurrashid Akanbi ya ce bautar gumaka an yita ne cikin jahilci a shekarun baya amma yanzu an samu ilimin da ya tabbatar da Allah daya ne.

Ya kuma kara da cewa ya rusa gunkin ne domin ya kare mutanensa daga afkawa duhun bautar gumaka zuwa hasken imani da Allah daya.

Dama Yarabawa na bautar Allah daya

Oba Abdurrashid Akanbi ya tabbatar da cewa tun asali Yarabawa an sansu ne da bautawa Allah shi kadai.

Ya ce iyayen Yarabawa tun daga kan Oduduwa zuwa Ogun da sauransu duk sun bautawa Allah ne shi kadai saboda haka zai bi hanyarsu.

Musulunci ne mafita ga Najeriya

Kara karanta wannan

'Kar ka fara da bada hakuri': 'Yan kasa sun yi martani ga Tinubu, sun fadi mafita ga Najeriya

Dangane da tarin matsalolin da Najeriya ke fama dasu, basaraken ya ce bin koyarwar Musulunci ne kawai mafita.

Oba Abdurrashid Akanbi ya ce ya kamata Najeriya ta yi koyi da ƙasar Saudiyya wajen bin Allah domin samun cigaban zamani da Saudiyya ta samu.

Basarake ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen mai sarautar gargajiya a Kudancin Najeriya, Oba Abdulrasheed Akanbi na Iwo ya yi alfahari kan 'yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa basaraken ya ce girman rawaninsa ya fi karfin wani dan bindiga da aka haifa ya kai masa farmaki a yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng