Matasan N Power Za Su Sha Jar Miya, Watakila Tinubu Zai Biya Su Basukan Watanni 8

Matasan N Power Za Su Sha Jar Miya, Watakila Tinubu Zai Biya Su Basukan Watanni 8

  • Da alamu matasa za su kwashe bayan Bola Tinubu ya juyo ta kansu kan basukan N-power da suke bin gwamnati
  • Matasa masu cin gajiyar N-power suna bin gwamnatin akalla basukan watanni takwas ba tare da biyansu ba
  • Ma'aikatar jin kai ta ce za su iya samun basukan da suke bi na watanni takwas a karshen wannan wata da muke ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan basukan masu cin gajiyar N-power a Najeriya.

Gwamnatin ta ce za ta iya biyan basukan da matasan ke binta na watanni takwas a karshen wannan wata.

Watakila masu cin gajiyar N-power za su iya samun basukansu a karshen wata
Matasan N-power suna bin gwamnati bashin watanni 8. Hoto: N-power.
Asali: Facebook

N-power: Sanarwa kan biyan basukan

Kara karanta wannan

"Jima'i kadai ke rage mana kunci": 'Yan gudun hijira sun cika sansani da jarirai

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da makarantar jin kai da walwala ta fitar a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Masu cin gajiyar N-power za su iya samun alawus da suke bin gwamnati na watanni takwas a karshen wannan wata, ku kara hakuri."

- Ma'aikatar jin kai

Tulin basuka da N-power ke bin gwamnati

Wannan na zuwa ne yayin da masu cin gajiyar N-power ke kokawa kan tulin basukan da suke bin gwamnatin a baya.

Akalla matasan na bin gwamnatin bashin watanni takwas wanda ba a biya su ba yayin da suke cikin shirin.

Daga bisani an dakatar da shirin kan binciken badakala a ma'aikatar da ake zargin Ministar jin kai, Dakta Betta Edu da mukarrabanta.

Daga bisani an dakatar Edu saboda kaddamar da bincike game da almundahana a ma'aikatar na biliyoyi.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yi albishir yayin da ta bayyana ƙoƙarinta wajen shawo matsalolin Najeriya

Gwamanti ta fara biyan N-power

Kun ji cewa Gwamnatin Tarayya karkashin shugaban ƙasa, Bola Tinubu ta tabbatar da cewa masu jin gajiyar N-Power cewa an fara angiza musu kuɗi.

Wannan na kunshe a wani sakon tabbatarwa da sashin kula da harkokin walwala (NASIMS) ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis 21 ga watan Disamba.

NASIMS ya bayyana cewa masu cin gajiyar N-Power na rukunin C2 ne kaɗai aka fara biya hakkokinsu da suka jima suna jira a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.