Duk da Ikirarin Gidansa 1 Tak, an Gano El Rufai Ya Mallaki Gidan $193,084 a Dubai

Duk da Ikirarin Gidansa 1 Tak, an Gano El Rufai Ya Mallaki Gidan $193,084 a Dubai

  • Wani bincike da masu shirin fallasa rashawa (OCCRP) tare da hadin guiwar jaridu 70 suka yi, ya nuna Nasiru El-Rufai ya mallaki gida a waje
  • Kamar yadda binciken ya nuna, El-Rufai na daga cikin manyan 'yan siyasa, sojoji, alkalai akalla 200 da aka gano sun mallaki kadaroi a Dubai
  • Abin mamaki, shekara daya kafin a fitar da wannan rahoton, tsohon gwamnan na Kaduna ya yi ikirarin cewa gida tak ya mallaka a rayuwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A ranar Litinin ne rahoto ya fita na jerin wasu manyan 'yan siyasar Najeriya (PEPs), da jami'an tsaro da suka mallaki kadarori masu tsada a kasar Dubai.

Ba iya 'yan siyasa ko jami'an tsaro ba, akwai sunayen iyalan 'yan siyasar, alkalan kotu, manyan ma'aikatan gwamnati da suka kai 200 a jerin mamallakan kadarori a Dubai.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Rahoto ya nuna cewa El-Rufai ya mallaki gida a Dubai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai. Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

'Yan Najeriya masu gida a Dubai

Kamar yadda rahoton jaridar BusinessDay ya nuna, wannan fallasar na daga cikin binciken ƙwaƙwaf da tawagar 'yan jaridu ke yi kan kadarorin da 'yan Najeriya suka mallaka a Dubai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rahoto da hukumar filaye ta Dubai ta fitar, ya nuna cewa 'yan Najeriya ne na biyu bayan kasar India da suka fi mallakar kadarori a kasar.

Atiku Abubakar, Nasiru El-Rufai, Lateef Olasunkanmi Fagbemi, Yusuf Datti Baba-Ahmed, Attahiru Bafarawa da sauran su, na a cikin wannan jerin sunayen.

Gidajen tsofaffin gwamnonin Kaduna a Dubai

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsofaffin gwamnonin Kaduna, Ahmed Makarfi da Nasiru El-Rufai na daga cikin wadanda rahoton ya ce sun mallaki gida a Dubai.

Yayin da aka ce Makarfi ya mallaki gida a Burj Khalifa mai darajar $822,016 (N1,258,416,074) an ce El-Rufai ya mallaki gidan da kudinsa ya kai $193,084 (N295,590,364) a Al Hebiah III.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Abin mamaki shi ne, shekara daya kafin a fitar da wannan rahoton, El-Rufai ya yi ikirarin cewa bai mallaki gida ko daya a wajen Kaduna ba, gidansa daya ne tak, kuma yana Kaduna.

"Gida na 1 rak a Kaduna" - El-Rufai

A wata tattaunawa da wani gidan rediyo, El-Rufai ya ce ko kadan bai taba daukar kudin jihar Kaduna ya kai su ketare ba.

Ya kuma ƙalubalanci wadanda suka gabace shi a shugabancin jihar, da su rantse da Allah cewa ba su saci kudin jihar Kaduna ba, kamar yadda rahoton PM News ya nuna.

Tsohon gwamnan na Kaduna ya ce:

"Ina alfahari da titunan da na shimfida wadanda za su dade ana mora. Ba mu kwashi kudin jiha mun tafi Dubai mun saye gida ba, kuma ba mu je titin Jabi mun gina gida ba.
"Na zama gwamnan Kaduna ne ina da gida daya wanda ke kan titin Unguwan Sarki, Kaduna. Na kammala mulkina, Alhamdulillah, wannan gidan ne kaɗai na mallaka."

Kara karanta wannan

Zambar Naira miliyan 22: EFCC ta cafke ma'aikacin karya a fadar shugaban kasa

Abba ya ba Aminu Bayero sabon umarni

A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ba Aminu Ado Bayero sabon umarni na ya gaggauta ficewa daga fadar Nasarawa.

Gwamnatin Kano ta ce abin takaici ne yadda har yanzu sarkin Kano na 15 ke ci gaba da zama a fadar duk da an ba shi umarni ya fita saboda za a yi gyara a ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.