Umahi: Ma'aikaciyar Jinya Ta Mutu a Gidan Ministan Tinubu, an Zarge Shi da Boye Gaskiya
- Ministan ayyuka, David Umahi, ya musanta zargin cewa an ɓoye gaskiya game da mutuwar wata ma'aikaciyar jinya a gidansa da ke jihar Ebonyi
- Ya ce iyalan marigayiyar ne suka balle ƙofar ɗakinta bayan sun damu da halin da take ciki, sannan suka garzaya da ita asibiti
- Umahi ya bayyana cewa an kai rahoton lamarin ga 'yan sanda, kuma za a gudanar da binciken gawar da amincewar iyayen marigayiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abakaliki, Ebonyi - Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi martani kan rahotannin da ke yawo game da mutuwar wata ma'aikaciyar jinya mai suna Mary Habila a gidansa da ke jihar Ebonyi.
Umahi ya yi wannan bayani ne ranar Lahadi, 12 ga watan Yulin 2026 yayin da yake duba ayyukan gina babbar hanyar Calabar–Ebonyi–Benue–Nasarawa–Abuja.

Source: Facebook
A cewarsa, iyalan marigayiyar ne suka fara shiga ɗakinta bayan sun damu da rashin jin duriyarta, kafin daga bisani su kai ta asibiti domin ceto rayuwarta, cewar rahoton jaridar The Cable.
Yadda aka kai lamarin ga 'yan sanda
Ministan ayyukan na Najeriya ya bayyana cewa an sanar da 'yan sanda cikin gaggawa bayan faruwar lamarin.
Ya ƙara da cewa ya ba da umarnin gudanar da binciken gawar domin gano ainihin musabbabin mutuwar, kuma za a yi hakan ne tare da amincewar iyayen marigayiyar.
Umahi ya musanta boye gaskiya
Umahi ya musanta zargin da ake yi cewa an yi ƙoƙarin ɓoye bayanai game da mutuwar Mary Habila, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
"Iyalan yarinyar ne suka balle ƙofar ɗakinta, suka kira likitoci daga David Umahi Federal University Teaching Hospital (DUFUTH), waɗanda suka kai ta asibiti kuma suka yi duk mai yiwuwa domin farfaɗo da ita, amma hakan bai yi nasara ba."
"Iyalan ne suka kai rahoton lamarin ga 'yan sanda. Don haka ina ne batun ɓoye gaskiya yake?"
- David Umahi
Umahi ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a
Ministan ya ce ya umarci lauyoyinsa su fara ɗaukar matakin shari'a a kan mutanen da ke yaɗa abin da ya kira rahotannin ƙarya game da mutuwar ma'ikaciyar jinyar.

Kara karanta wannan
"Shin Rasha ta kashe sanatan Amurka"; An fara nuna yatsa kan mutuwar aminin Trump
Ya bayyana marigayiyar a matsayin ma'aikaciya mai ƙwazo a David Umahi Federal University Teaching Hospital (DUFUTH).

Source: Twitter
Umahi ya kuma ce iyayen marigayiyar, waɗanda ke jihar Ebonyi a halin yanzu, za su gana da manema labarai domin yin bayani kan lamarin, sannan su ma su ɗauki matakin shari'a a kan masu yaɗa abin da suka bayyana a matsayin ƙarya.
Umahi ya ce ya fi karfin Peter Obi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan ayyuka, David Umahi, ya yi watsi da tasirin siyasar Peter Obi, yana mai cewa tsohon gwamnan Anambra ba barazana ba ne ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko Jam'iyyar APC.
David Umahi ya ce shi kansa ba ya tsoron Peter Obi, balle kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko jam'iyyar APC, ya nuna cewa Obi ya san ba zai iya fafatawa da shi ba.
Ministan ayyukan ya kuma soki tarihin mulkin Peter Obi a Anambra, ya tambayi irin nasarorin da ya samu lokacin yana gwamna.
Asali: Legit.ng
