Marigayi Ibrahim Lamorde: Abubuwa 5 da Ba Ku Sani Ba Kan Shugaban EFCC da Ya Rasu

Marigayi Ibrahim Lamorde: Abubuwa 5 da Ba Ku Sani Ba Kan Shugaban EFCC da Ya Rasu

  • A ranar 25 ga watan Mayu ne tsohon shugaban hukumar EFCC Ibrahim Lamorde ya rasu bayan fama da jinya da ya yi a kasar waje
  • Ibrahim Lamorde ya rike mukamai da dama a hukumar EFCC kafin shugaba Goodluck Jonathan ya nada shi shugaban hukumar
  • A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa masu muhimmanci da suka shafi rayuwar Ibrahim Lamorde da baku sani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

A ranar 25 ga watan Mayu ne tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya.

iBRAHIM LAMORDE
Ibrahim Lamorde ya dawo da kudin Abacha da kama tsohon gwamna a lokacinsa. Hoto: @Shangudar.
Asali: Twitter

Rahoton jaridar Premium Times ya nuna cewa Ibrahim Lamorde ya rasu ne bayan jinya da ya yi a kasar Masar.

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya yi alkawura kan inganta rayuwar kananan yara

A wannan rahoton, Legit ta tatttaro muku abubuwa biyar masu muhimmanci kan rayuwar Ibrahim Lamorde.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. An haifi Ibrahim Lamorde a Mubi

An haifi Ibrahim Lamorde a karamar hukumar Mubi da ke jihar Adamawa a Arewa maso gabashin Najeriya.

Haihuwarsa ta zo daidai da ranar 20 ga watan Disambar shekarar 1962 kuma ya tashi ne a garin na Mubi.

2. Lamorde ya yi karatu a ABU Zariya

Ibrahim Lamorde ya samu damar shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin yin digiri na farko.

Ya kuma kammala jami'ar ta ABU a shekarar 1984 in da ya karanci ilimin sanin halayyar dan Adam.

3. Marigayi Lamorde da aikin dan sanda

Shekaru biyu bayan kammala karatun jami'a, Ibrahim Lamorde ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1986.

Ya rike mukamai da dama a aikin da ya yi da rundunar yan sanda ta kasa kafin ya yi ritaya a shekarar 2021.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Tsohon shugaban hukumar EFCC, Lamorde ya rasu yana da shekaru 61

4. Lamorde ya zama shugaban EFCC na 3

Ibrahim Lamorde shi ne shugaban hukumar EFCC na uku wanda shugaba Goodluck Jonathan ya nada shi a shekarar 2011 bayan sauke Farida Waziri.

Har ila yau shugaba Muhammadu Buhari ya sauke Ibrahim Lamorde daga shugabancin EFCC a shekarar 2015 inda ya nada Ibrahim Magu shugaban riko na hukumar.

5. EFCC: Lamorde ya daure tsohon gwamna

A tarihin aiki da ya yi a EFCC, Ibrahim Lamorde ya yi yaki da cin hanci da rashawa har ya yi sanadiyyar daure tsohon gwamnan jihar Delta, rahoton Vanguard.

A lokacinsa ne aka kama tsohon gwamna James Ibori kuma har ila ya dawo da dala biliyan 1 ga Najeriya cikin kudin da ke zargin Abacha da boyewa a kasashen Turai.

EFCC ta kama Hadi Sirika

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC mai yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta kama tsohon ministan Muhammadu Buhari, Hadi Sirika.

Kara karanta wannan

"Babu mai daƙile mani hanyar abinci", Shugaban karamar hukuma ya gargadi gwamna

EFCC ta kama Hadi Sirika bisa zargin sa da hannu cikin badakallar kudi sama da Naira biliyan takwas a lokacin da yake minista a gwamnatin tarayya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel