Zanga Zanga Ta Barke: Iyayen Daliban Borno Sun Dura kan Tinubu bayan Ceto na Oyo

Zanga Zanga Ta Barke: Iyayen Daliban Borno Sun Dura kan Tinubu bayan Ceto na Oyo

  • Iyalan ɗaliban makarantar firamaren Mussa sun ce watanni biyu bayan sace 'ya'yansu, har yanzu babu wani bayani kan inda suke ko halin da suke ciki
  • Iyayen sun buƙaci gwamnatin tarayya ta nuna irin ƙoƙarin da ta yi wajen ceto ɗaliban Oyo domin kubutar da waɗanda aka sace a makarantar Borno
  • Matasa da ɗalibai sun gudanar da zanga-zangar lumana a Maiduguri, suna kira ga gwamnati ta ceto ɗaliban Mussa, Lassa da sauran yankunan Borno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Iyalan ɗaliban da aka sace daga makarantar firamare da sakandiren Mussa da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba a jihar Borno sun mika kokensu ga gwamnati.

Iyalan sun roƙi gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi wajen ceto 'ya'yansu, suna mai cewa sun ji an yi watsi da su watanni biyu bayan faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano wasu ƴan ta'addan ƙasashen waje a Borno, sun karya lagon ISWAP

Iyalai sun nemi gwamnati ta ceto daliban Borno kamar yadda aka ceto daliban Oyo
Wasu matasa sun gudanar da zanga zanga doin a ceto daliban Borno da aka sace. Hoto: @Onsogbu
Source: Twitter

Iyalan yaran da aka sace a Borno sun magantu

Kiran nasu ya zo ne kwanaki kaɗan bayan jami'an tsaro sun ceto malamai da ɗaliban da aka sace daga makarantu uku a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo, a cewar rahoton Daily Trust.

Duk hare-haren biyu sun faru ne a ranar 15 ga Mayun 2026, inda aka yi garkuwa da sama da ɗalibai da malamai 40, ciki har da ƙananan yara masu shekara biyu a makarantar Mussa.

Shugaban kwamitin iyaye, Ishaku Suya, ya shaida wa jaridar cewa tun bayan ziyarar da kwamishinan ilimin Borno ya kai musu tare da alƙawarin ceto waɗanda aka sace, ba su sake jin wani sabon bayani ba.

Iyalai sun koka ga gwamnatin tarayya

Ya ce sun yi farin cikin jin an ceto ɗaliban Oyo, amma suna ganin an manta da 'ya'yansu. Wani uba mai suna Sale Buba ya ce rashin sanin inda yaran suke da halin da suke ciki ya jefa iyalai cikin damuwa.

Kara karanta wannan

Dalibai da malaman da aka sace a Oyo sun kubuta, an samu bayanai

Ita ma Ishaku Joe ta ce shiru da aka yi kan lamarin ya ƙara musu raɗaɗi, yayin da wani mahaifi mai suna James ya bayyana cewa abin takaici ne gwamnati ta bar su cikin wannan hali duk da alhakin da ke kanta na kare rayukan 'yan ƙasa.

Matasa sun gudanar da zanga zanga a Borno kan matsalar tsaro
Taswirar jihar Borno, inda matasa suka gudanar da zanga zanga kan matsalar tsaro. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Matasa sun yi zanga-zanga a Maiduguri

A wani ɓangaren kuma, jaridar Punch ta ruwaito cewa haɗakar matasa da ɗalibai ta gudanar da zanga-zangar lumana a Maiduguri domin nuna damuwa kan matsalar tsaro tare da neman a ceto ɗaliban da aka sace.

Jagoran zanga-zangar, Suleiman Muhammed, ya yaba da nasarar ceto ɗaliban Oyo, amma ya buƙaci gwamnati ta yi irin wannan ƙoƙari domin kuɓutar da ɗaliban Mussa, Lassa da sauran al'ummomin Borno da har yanzu suke hannun masu garkuwa da mutane.

An nemi Tinubu ya ceto daliban Arewa

A wani labari, mun ruwaito cewa, masanin tsaro kuma mai fafutukar kare hakkin dan adam, Barista Bulama Bukarti ya yaba da dabarun da aka yi amfani da su a ceto daliban Oyo.

Barista Bulama Bukarti ya bayyana cewa wannan ya kara haska bukatar da ake da shi a kan wasu dalibai a Arewacin Najeriya da aka sace a lokaci guda da na jihar Oyo.

Mai rajin kare hakkin dan Adam din ya bukaci 'yan Najeriya su ci gaba da matsa wa gwamnati lamba domin tabbatar da cewa daliban sun kubuta daga hannun yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com