Fitaccen Malamin Addini, Alkali Abubakar Zariya Zai Ƙara Aure, Ya Fadi Sunan Amaryarsa

Fitaccen Malamin Addini, Alkali Abubakar Zariya Zai Ƙara Aure, Ya Fadi Sunan Amaryarsa

  • Shehin malamin addinin Musulunci a Arewa, Alkali Abubakar Salihu Zariya ya ce maganar ƙara aure da zai yi na nan daram dam
  • Alkali Abubakar Zariya ya ce soyayya da yabon da ya ke yi wa matarsa Hajiya Jamila ba shi zai hana ya auri sahibarsa Sumayya ba
  • Shehin malamin ya kuma yi martani ga 'yan soshiyal midiya da ke ta faman ce-ce-ku-ce kan batun auren nasa da Hajiya Sumayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna- Fitaccen malamin addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya, Alkali Abubakar Salihu Zariya ya yi magana kan shirin ƙarin auren da ya ke yi.

Alkali Abubakar Zariya ya yi magana kan karin aure
Ustaz Abubakar Salihu Zariya ya jadda cewa zai kara aure duk da yana kaunar Jamila. Hoto: Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria
Asali: Facebook

Alkali Abubakar Zariya ya ce soyayya da yabon da yake yi wa uwar gidansa, Jamila, ba shi zai hana ya auri masoyiyarsa Sumayya ba.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rigimar sarautar Kano, Sarki Sanusi II ya faɗi abin da zai kawo ci gaba a ƙasa

Dalilin da ya sa malamin zai kara aure

A wata hira da gidan rediyon Freedom da ke Kano, malamin addinin ya ce masu cece-kuce a kan ƙarin auren sun daɗe, domin ba gudu ba ja da baya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ya na kyautata zaton ƙarin auren zai ragewa Jamila ayyukan cikin gida, haka zalika ba za ta yi zaman mokoki ita kadai idan ya koma ga mahaliccinsa ba.

A bangarensa shi ma, idan Allah SWT ya fara karbar rayuwar Jamila, zai samu saukin raɗaɗin mutuwar saboda yana da Sumayya.

"Karin aure na nan ba fashi" - Alkali

A cewar Alkali Abubakar Zariya:

"Yabon da nake yi wa Hajiya Jamila ba zan daina ba, haka kuma ƙarin auren ba zan fasa ba sai idan na mutu.
"Rubuce rubucen da 'yan soshiyal midiya suke yi a kan aure na ba zai canja komai ba, kuma ita Hajiya Jamila ta na yin kishi ne irin wanda shari'a ta yarda da shi."

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Saurari tattaunawar a kasa:

Dahiru Bauchi ya aika wa Abba sako

A wani labarin, mun ruwaito cewar babban malamin addini, Sheikh Dahiru Bauchi ya nemi gwamnan Kano Abba Yusuf da ya mutunta umarnin kotu.

Sheikh Dahiru Bauchi na magana ne kan rigimar da ta kaure a jihar kan batun nadin sabon sarki da aka yi, wanda ya sa babbar kotun tarayya ta dakatar da nadin amma Abba bai ji ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel