Allah Mai Iko: Yadda ’Yar Najeriya Ta Haifi ’Yan 4 Bayan Shekara 18 da Yin Aure

Allah Mai Iko: Yadda ’Yar Najeriya Ta Haifi ’Yan 4 Bayan Shekara 18 da Yin Aure

  • Wani dan Najeriya ya ba da labarin yadda wata mata ‘yar kasar ta haifi ‘ya’ya hudu bayan daukar dogon lokaci ta na jira
  • A cikin labarin da ya bayar, ya bayyana cewa matar ta haifi ‘yan hudun ne a rana daya bayan ta shafe shekaru 18 ba haihuwa
  • Masu amfani da shafukan sada zumunta sun shiga sashin sharhi na bidiyon da mutum ya wallafa domin taya matar murna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

'Yan uwa, abokan harziki da ma ma'abota shafukan yanar gizo sun cika da farin ciki bayan wata ‘yar Najeriya ta haifi ‘yan hudu.

An tattaro cewa matar ta shafe tsawon shekaru kusan 18 ba tare da ta yi ko barin ciki ba, lamarin da ya jefa ta a damuwa, amma ta ci gaba da zaman jira.

Kara karanta wannan

Diyar Ado Bayero ta turawa Tinubu da Abba sako, tayi zancen rigimar masarautar Kano

Wata 'yar Najeriya ta haifi 'yan hudu bayan shekara 18
Mutane sun yi tururuwar taya 'yar Najeriya murnar haihuwar 'yan 4. Hoto: @azalina58
Asali: TikTok

Jama'a sun taya uwar 'yan 4 murna

A cikin faifan bidiyon da wata mata mai suna @azalina58 ta wallafa a Tik Tok, shaidun gani da ido sun yi tsalle don murna tare da taya matar farin ciki sosai kan karuwar da ta samu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An dai ga uwar 'yan hudun kwance a kan gado ita ma tana murna yayin da jama'ar da ke tare da ita ke ci gaba da godewa Allah kan ganin wannan rana.

@azalina58 ta wallafa cewa:

"Muna murna mama ta haifi yara hudu, maza biyu mata biyu bayan shafe shekaru 18 ta na jira. Lallai muna cike da farin ciki, kuma muna taya mamanmu murna."

Kalli bidiyon a kasa:

'Yan soshiyal midiya sun yi murna

Masu amfani da shafukan sada zumunta sun shiga sashin sharhi na bidiyon da mutum ya wallafa domin taya matar murna.

Kara karanta wannan

Barauniya ta raba mai jego da jaririn wata 1, ta fada hannun jami'an tsaro

@Komai_Amanda ya ce:

"Muna taya ki murna sosai, yanzu abin da ya rage shi ne muyi fatan ki ba 'ya'yan ki tarbiya mai kyau."

@ESOSA ya ce:

"Amma har yanzu wasu ke ganin babu ubangiji?"

@Peculiar ya ce:

"Yanzu ta ina kimiyya za ta fara bayanin yadda matar ta haihu bayan shekaru 18? Ai sai dai mu taya ta murna kawai."

Haka dai jama'a su ke ta maganganu ire-iren wadannan dai sauran su.

'Yar shekara 70 ta haifi tagwaye

A wani labarin, mun ruwaito cewa wata dattijuwa mai shekara 70 ta haifi tagwaye a wani asibitin karbar haihuwa da kula da mata na kasa-da-kasa da ke Uganda.

An tattaro cewa asibitin ya yi amfani da fasahar IVF wajen karbar haihuwar, inda dattijuwar ta zama mace ta farko a Afrika da ta haihu bayan shekaru 70 ta hanyar IVF.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel