Yajin Aiki: Fitaccen Mawaƙin Najeriya, Falz, Ya Tafka Asarar Miliyoyin Naira a Awa 48
- Yajin aikin kasa da awanni 48 da 'yan kwadago suka yi a Najeriya ya shafi fitaccen mawaki Folarin Falana, wanda aka fi sani da Falz
- Falz ya ce ya yi asarar dukkanin kudin da ya kashe wajen shirya daukar wani bidiyo saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo
- Sai dai mawakin ya ce ya fahimci dalilan yin yajin aikin, inda ya kara da cewa yana goyon bayan bukatun kungiyoyin kwadagon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Uyo - Fitaccen mawakin Najeriya, Folarin Falana, wanda aka fi sani da Falz, ya bayyana yadda yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi ya sa ya yi asarar kudi masu yawa.
Falz ya ce ya yi asarar dukkanin kudin da ya kashe wajen shirya daukar wani bidiyon wakarsa saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo.
Mawaki ya yi asara saboda yajin-aiki
Da yake magana a wani sakon bidiyo wanda shafin Abuja Gist ya wallafa a Instagram, Falz ya bayyana cewa yajin aikin ne ya sa ya makale a garin Uyo saboda an rufe filayen jiragen sama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai mawakin ya ce ya fahimci dalilan gudanar da yajin aikin, inda ya kara da cewa yana goyon bayan bukatun kungiyoyin kwadago, in ji rahoton jaridar The Nation.
"Ina goyon bayan 'yan kwadago" - Falz
Falz ya ce:
“Na farka da safiyar yau, na tashi da zummar zuwa filin jirgi kawai sai na ji labarin an rufe filin jirgin, an soke dukkanin tashin jirage saboda yajin aiki.
"Akwai bidiyon da ya kamata in yi a Legas yau amma na makale a Uyo, na yi asarar kudi masu yawa saboda mun riga mun biya kudin ajiyar wasu kaya, yanzu dole mu sake biya.
"Duk da cewa yajin aikin ya shafe ni sosai, amma na fahimci dalilin yin shi kuma ina tare da su. Ina tare da 'yan kwadago domin tuntuni ya kamata ayi hakan."
'Yan kwadago sun shiga yajin aiki
A iya tunawa a baya mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadagon Najeriya, NLC da TUC sun tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya daga Litinin.
Sun shiga yajin aikin ne domin tilastawa gwamnati amincewa da sabon mafi karancin albashin ma’aikata tare da sake duba karin farashin wutar lantarki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng