Shiri Ya Kankama: Tinubu Zai Yi Wani Babban Aiki na Naira Tiriliyan 1.05 a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi tawagar MOFI da Mota-Engil domin tattauna shirye-shiryen fara aikin layin dogo na Kano mai darajar tiriliyan 1.05
- Gwamnan ya ce aikin zai inganta sufuri, rage cunkoso da ƙarfafa harkokin kasuwanci tare da bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano
- Abba Yusuf ya yabawa Shugaba Bola Tinubu da Hon. Abubakar Kabir Bichi saboda rawar da suka taka wajen tabbatar da amincewa da aikin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin tawaga daga hukumar kamfanonin kudi ta MOFI da kamfanin Mota-Engil Nigeria.
An kai ziyarar ne gabanin bikin aza harsashin aikin layin dogon jirgin ƙasa na Kano mai darajar tiriliyan 1.05, wanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da shi kwanan nan.

Source: Facebook
An fara shirin gina layin dogon Kano
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar a shafinsa na Facebook.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Manajan Daraktan MOFI, Dakta Armstrong Ume Takang, da Shugaban Mota-Engil Nigeria, Mista Kola Karim, ta gana da gwamnan a masaukin gwamnatin jihar Kano da ke Asokoro a Abuja.
A yayin ganawar, sun yi wa gwamnan bayani kan shirye-shiryen da ake yi domin fara aiwatar da aikin.
A cikin sanarwar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce ana sa ran aikin layin dogon jirgin ƙasan mai darajar tiriliyan 1.05 zai kawo sauyi mai ma'ana a harkar sufurin birane a Kano.
Sanarwar ta bayyana cewa aikin zai inganta haɗa yankuna da juna, rage cunkoson ababen hawa, tare da ƙarfafa harkokin tattalin arziki a faɗin jihar.
Gwamna Abba ya yaba wa Tinubu
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da aiki tare da gwamnatin tarayya da kamfanonin da ke gudanar da aikin domin tabbatar da an kammala wannan babban shiri cikin nasara.
Ya ce aikin wani muhimmin zuba jari ne da zai ƙara tabbatar da matsayin Kano a matsayin cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya, tare da samar wa mazauna jihar ingantaccen tsarin sufurin jama'a mai aminci da inganci.
Gwamnan ya kuma miƙa godiyarsa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa amincewa da aikin, yana mai cewa wannan mataki zai taimaka wajen hanzarta bunƙasar tattalin arziki da ci gaban zamantakewar jihar.

Source: Facebook
Layin dogo zai karfafa kasuwanci
Hakazalika, ya yabawa shugaban kwamitin kasafin kuɗi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Bichi, saboda goyon bayan da ya bayar a fannin dokoki, wanda ya taimaka wajen ganin aikin ya samu damar kankama.
Ana sa ran idan aka kammala aikin layin dogon jirgin ƙasan na Kano, zai sauƙaƙa zirga-zirga a faɗin jihar, ya ƙarfafa harkokin kasuwanci tare da inganta tsarin sufuri baki ɗaya.
An ware $1.3bn kan layin dogon Kano-Maradi
A wani labari, mun ruwaito cewa, a kokarin Gwamnatin Tarayya wurin inganta sufuri, ta yi nasarar samun $1.3bn domin karasa aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi.
Ministan sufuri a Najeriya, Sanata Sa’idu Alkali ya bayyana haka ga ‘yan jaridu inda ya ce hanyar za ta bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu.
Tun a mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne aka kaddamar da gina haryar jirgin kasa ta Kano-Katsina-Jibiya zuwa Maradi.
Asali: Legit.ng

