Jerin Mutum 10 da Suka Fi Kowa Arziki a Duniya da Adadin Dukiyar da Suka Mallaka

Jerin Mutum 10 da Suka Fi Kowa Arziki a Duniya da Adadin Dukiyar da Suka Mallaka

 • Jerin manyan attajirai na duniya ya sake canzawa, inda yanzu Jeff Bezos ke rike da kambun mafi arziki a duniya
 • Bezos ya hambare hamshakin attajirin nan dan kasar Faransa Bernard Arnault bayan da arzikinsa ya karu da dala miliyan 75
 • Attajirin Najeriya, Aliko Dangote, shi ma ya kara samun matsayi a cikin jerin attajiran bayan ya samu ribar biliyoyi a cikin sa’o’i 24

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jeff Bezos ya sake zama mutumin da ya fi kowa kudi a duniya, inda ya kwato matsayi na daya daga hannun hamshakin attajirin nan dan kasar Faransa Bernard Arnault.

Bayani kan mutane 10 mafi arziki a duniya
Jeff Bezos ya sake zama mutumin da ya fi kowa arziki a duniya. Hoto: Stefano Rellandini, Elon Musk/X, Dangote Group/X
Asali: Getty Images

Bezos ya fi kowa kudi a yau

A cewar kididdigar Bloomberg Billionaires, dukiyar Bezos ta kai dala biliyan 201 bayan samun sama da dala miliyan 75 (N105.82bn) a ranar Alhamis, 21 ga Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Kano: Daina amfani da soshiyal midiya da wasu sharuɗa da kotu ta kafawa Murja Kunya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kididdigar ta kuma bayyana cewa daga watan Janairu zuwa 22 ga Maris, wanda ya kafa Amazon ya samu ribar dala biliyan 24.

A baya-bayan nan ne Legit.ng ta rahoto cewa Jeff Bezos ya zarce Elon Musk a matsayi na farko tun 2021.

Mutum na 2 mafi arziki a duniya

Bisa kididdigar da aka yi, Bernard Arnault, babban jami'in kula da kayayyakin alatu na kamfanin Louis Vuitton, yanzu ya zama mutum na biyu mafi arziki da dukiyar da ta kai dala biliyan 198.

An hambarar da shi ne bayan da dukiyarsa ta yi kasa da dala miliyan 931 a cikin sa'o'i 24.

A bangaren Elon Musk, dukiyarsa ta ragu da dala biliyan 2.03 a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda ya jawo shi kusa zuwa matsayi na 4.

Kara karanta wannan

Sahun mutane 2 rak da Musulunci ya halattawa ciyarwa a maimakon yin azumi

Jerin mutane 10 mafi arziki a duniya

 1. Jeff Bezos - $201bn
 2. Bernard Arnault - $198bn
 3. Elon Musk - $187bn
 4. Mark Zuckerberg - $180bn
 5. Bill Gates - $154bn
 6. Steve Ballmer - $148bn
 7. Larry Ellison - $141bn
 8. Warren Buffett - $137bn
 9. Larry Page - $134bn
 10. Sergey Brin - $127bn

Matsayin Dangote a attajiran duniya

A bisa kididdigar Bloomberg, Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka har zuwa ranar 22 ga Maris, 2024, ya mallaki dalar Amurka biliyan 15.7.

Ya samu ribar dala miliyan 624 a cikin sa’o’i 24, inda ya zarce attajirai tara, kuma a yanzu ya zama mutum na 126 mafi arziki a duniya.

Matsayin arzikin Najeriya a idon duniya

A wani rahoton, Legit Hausa ta ruwaito cewa an nemi sunan Najeriya an rasa a jerin ƙasashe 10 mafi karfin tattalin arziki a Afrika.

Wannan na nufin cewa, Najeriya ta gaza samun gurbin gogayya da Moroko don samun matsayi a jerin goman farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel