Baraya: 'Yadda Gwamnatin Kano Ta Kori 'Yan Kwankwasiyya kusan da 350 daga Aiki'

Baraya: 'Yadda Gwamnatin Kano Ta Kori 'Yan Kwankwasiyya kusan da 350 daga Aiki'

  • Barayan Karaye da ya ke takarar majalisar jiha a Kano ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da korar sama da 'yan Kwankwasiyya 300 daga aiki
  • Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya kara da cewa haka kuma soke sunayen wasu da aka ba kujerar aikin Hajji saboda su na tare da Kwankwasiyya
  • Ya bayyana cewa sun karɓi ƙorafe-ƙorafe daga waɗanda abin ya shafa, kuma za su ɗauki mataki domin su ma yan Kano ne da su ke da hakkin samun aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Dan takarar Majalisar Jihar Kano a inuwar jam'iyyar NDC, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye, ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da raba 'yan Kwankwasiyya da aikin da suke samun abincinsu.

Ya bayyana cewa a yanzu haka, gwamnatin Jihar Kano ta kori wasu daga cikin 'yan Kwankwasiyya da aka ba wa aikin koyarwa a tsarin BESDA.

Kara karanta wannan

'Gwamnatin yaudara ce': Barayan Karaye ya ce NDC ba ta fargabar Abba a zaben 2027

Barayan Karaye ya ce za su hukunta gwamnatin Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye Hoto: Hon Salisu Muhammad Kosawa/Barayan Karaye
Source: Facebook

A hira da ya yi da Legit, Ibrahim Abdullahi Karaye, wanda aka fi sani da Barayan Karaye, ya yi zargin cewa matasan da aka ɗauka aiki sannan aka kore su daga baya sun haura 300.

Adadin 'yan Kwankwasiyya da suka rasa aiki

A hirar da aka yi da shi, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara da cewa haka kuma gwamnatin Kano ta soke sunayen wasu 'yan Kwankwasiyya da aka ba kujerar aikin Hajji.

A kalamansa:

"A ka'idar aiki bai kamata a ce sai kana jam'iyya za a ɗauke ka aiki ba. An ɗauki wasu a BESDA, wasu an ɗauke su aiki na dindindin, amma yanzu an je an cire wajen mutum 350 kawai saboda su 'yan Kwankwasiyya ne."

Baraya, wanda ke takara a NDC ya bayyana cewa abin mamaki ne yadda gwamnati za ta siyasantar da aikin matasan Kano waɗanda suka cancanci a ba su aiki ba tare da nuna bambanci ba.

Kara karanta wannan

An kama matashi da buhunan abinci da wasu muhimman kaya zai kai wa Boko Haram

'Yan Kwankwasiyya sun kai ƙorafi

Ibrahim Abdullahi Karaye ya ƙara sanar da Legit cewa sun samu ƙorafe-ƙorafe daga matasan da aka kora daga bakin aiki, kuma za su ɗauki mataki.

Ya kara da cewa:

"Sun kawo mana takardarsu ta ƙorafi, kuma muna nan za mu ɗauki matakan da suka dace, ba za mu bar wannan abu haka ba."

Barayan Karayen ya kuma ce yanzu haka an tilastawa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo motar da aka ba shi ya na ofis.

Ya ce siyasa micijin gaske ne ba wasa ba, kuma za su hukunta duk wanda ya yi masu ba dai-dai ba idan lokacin hakan ya yi

Dan Kwankwasiyya ya soki gwamnati

A baya, mun kawo labarin cewa 'dan takarar majalisar jihar Kano na NDC, Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye, ya zargi gwamnatin Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen aiwatar da ayyukan raya kasa.

Ya ce gwamnati na amincewa da ayyuka ne kawai, amma ba a ganin aiwatar da su a ƙasa lamarin da ya sa babu abin da za a daga wajen kamfen a babban zaben 2027 da ke tafe a cikin yan watanni masu zuwa.

Injiniya Ibrahim Abdullahi Karaye ya kuma bayyana cewa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya fi Abba Kabir Yusuf ƙwarewa da gogewa a siyasa domin ya rike mukamai da ayyuka da gwamna bai yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng