'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Kwaleji, an Yi Awon Gaba da Dalibai
- An ce wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace ɗalibai takwas na Gateway ICT Polytechnic a jihar Ogun
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne bayan da maharan suka kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a Ipara
- Hukumar makarantar ta soke jarabawar da aka shirya yi bayan aukuwar lamarin na sace dalibai da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Ogun - An ce wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace ɗalibai takwas na Gateway ICT Polytechnic, Saapade (GAPOSA).
'Yan bindigan sun sace daliban ne bayan sun kai hari gidan da ɗaliban ke zaune a Ipara, ƙaramar hukumar Remo ta Arewa ta jihar Ogun.

Source: Original
Wani ɗalibi a makarantar da ya yi magana da jaridar Tribune Online bisa sharadin a sakaya sunansa ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Laraba, 29 ga watan Yulin 2026.
Majiyar ta ce masu garkuwar sun tafi da ɗalibai takwas a yayin harin da suka kai a gidan da daliban suke zaune.
Makaranta ta soke jarabawa
Bayan aukuwar lamarin, an ce hukumar makarantar ta sanar da soke jarabawar kwamfuta da ta rubutu da aka shirya gudanarwa a ranar Alhamis.
A wata sanarwa da hukumar makarantar ta fitar, ta bayyana cewa:
“SANARWA GA DUKKAN ƊALIBAI. Bayan mummunan lamarin da ya faru jiya, an soke jarabawar yau."
"Sai dai za a gudanar da jarabawar gobe kamar yadda aka tsara. Idan aka samu wani sauyi game da jarabawar gobe, za a sanar da ɗalibai cikin gaggawa."
"A yanzu, ana ƙarfafa dukkan ɗalibai su kwantar da hankulansu, su kasance masu kyakkyawan fata tare da ci gaba da shirye-shiryen jarabawarsu. Muna fatan za a warware lamarin cikin gaggawa. Mun gode da fahimta da haɗin kai.”
’Yan sanda sun tura jami’ai
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Ogun, DSP Oluseyi Babaseyi, ya tabbatar wa jaridar cewa sun samu rahoton sace wasu mutane a yankin Ipara. Sai dai kakakin ’yan sandan bai tabbatar da adadin mutanen da aka sace ba.
DSP Oluseyi Babaseyi ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya ta tura jami’anta yankin cikin gaggawa, musamman jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane da sashen yaƙi da manyan laifukan tashin hankali da sauran rundunonin musamman.

Source: Twitter
Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na makarantar, ya yi alƙawarin sake tuntuba domin yin ƙarin bayani kan lamarin.
Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ba a samu ƙarin bayani daga hukumar makarantar ba.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka akalla mutum bakwai a wani harin ta'addanci da suka kai hari a jihar Sokoto
Hatsabiban 'yan bindigan sun kai harin ne a ƙauyen Tsamaye da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.
Asali: Legit.ng

