Yadda Kasar UAE Ta Rika Sakin Bama Bamai a Iran Ta Bayan Fage
- An rawaito cewa kasar UAE ta kai hare-haren soji kan Iran, kamar yadda wasu majiyoyi masu masaniya kan lamarin suka bayyana
- Lamarin ya sanya kasar cikin ƙasashen da ke yaƙi kai tsaye a rikicin da Iran ta gwabza da Amurka da Isra'ila na kwana 40 Gabas ta Tsakiya
- Sojojin UAE na da kayan yaƙi na zamani da suka haɗa da jiragen yaƙi da aka ƙera a ƙasashen yamma da kuma tsarin sa ido na zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Wani rahoton ya ce kasar UAE ta kai hari kan wata matatar mai da ke tsibirin Lavan na Iran a farkon watan Afirilun shekarar 2026.
Ana cigaba da samun bayanai game da yakin da aka yi a Gabas ta Tsakiya bayan Amurka da Iran sun yi alkawarin tsagaita wuta a kwanakin baya.

Source: Getty Images
Wasu majiyoyi da ba a bayyana sunayensu ba ne suka shaida wa jaridar The Wall Street Journal cewa UAE ta kai hare-hare Tehran.
Harin da kasar UAE ta kai Iran
An ce an kai harin kan matatar ne a lokacin da shugaban Amurka, Donald Trump ke shirin sanar da tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran, wanda ya haddasa wata babbar gobara tare da dakatar da ayyukan matatar.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan UAE da Kuwait. Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce Amurka ta yi maraba da shigar UAE cikin yaƙin a boye.
Jaridar ta ce Iran ta kai wa UAE hare-hare fiye da kowace ƙasa, har da Isra’ila, inda ta kai fiye da hare-hare 2,800 ta hanyar makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa.
An ce hare-haren sun janyo babbar illa ga tattalin arziƙin UAE, inda suka haddasa sallamar ma’aikata da dakatar da wasu daga aiki.

Source: Getty Images
Kasar UAE ba ta yi martani ba
Ma’aikatar harkokin wajen UAE ba ta yi tsokaci kai tsaye kan hare-haren ba lokacin da jaridar ta nemi bayani. Sai dai ta yi nuni da wata sanarwa da ta fitar a baya wadda ta jaddada haƙƙin Abu Dhabi na mayar da martani ga duk wani hari.
Anadolu Agency ta wallafa cewa Dina Esfandiary da ke sharhi kan Gabas ta Tsakiya ta ce:
“Yana da muhimmanci a ga wata ƙasar Larabawan Gulf ta shiga yaƙi kai tsaye da Iran,”
“Yanzu Tehran za ta yi ƙoƙarin ƙara raba kan UAE da sauran ƙasashen Gulf waɗanda ke ƙoƙarin shiga tsakani domin kawo ƙarshen yaƙin.”
Mai goyon bayan Isra'ila ya mutu
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani dan kasar Amurka da ke rajin kare Isra'ila da Benjamin Netanyahu ra rigamu gidan gaskiya.
Mutumin mai suna Abraham Foxman ya kasance mai kare hare-haren da Isra'ila ke kai wa kasashe, musamman kan Falasdinawa a Gaza.
Makonni kafin Foxman ya mutu ya yaba wa shugaban Amurka, Donald Trump da Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan kai hari Iran.
Asali: Legit.ng

