Latest
Tsohon gwamnan Bayelsa, Kyaftin Olubolade, ya rasu yana da shekaru 70 a Legas bayan ya yanke jiki ya fadi a wajen wasan ƙwallon teburi. An yi jimamin rasuwarsa.
Rikici ya barke a jami'ar Katsina kan zaɓen VC. 'Yan takara sun soki zaɓen, sun zargi shugaba mai barin gado da nuna son zuciya domin wanda yake so ya samu nasara.
Maganar da jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya yi kan masu barin Kwankwasiyya ba ta yi wa tsagin Major Agɓo daɗi ba, ya maida masa da martani.
Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano ta rasa daya daga cikin mambobonta a majalisar dokokin jihar. Ya bayyana cewa rikicin jam'iyyar ya sanya ya fice daga cikinta.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya bayyana cewa jam'iyyun siyasa kamar APC da PDP ba su da bambanci domin duk manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.
Za ku ji a wannan rahoto cewa yan ta'addan Boko Haram na kwace makaman sojoji da aka sayawa da jami'an tsaro masu yawa, inji Dan majalisar Filato, Yusuf Gadgi.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hadu da shugaban gwamnonin Arewa a filin jirgin sama a jihar Kano. Kwankwaso ya kai ziyarar duba aiki a jihar Kano.
Barazanar Bello Turji ta tilasta mazauna Sokoto da Zamfara barin gidajensu yayin da hare-haren 'yan bindiga ke kara kamari a kauyuka daban-daban na jihohin.
An shiga jimami a jihar Bauchi bayan samun labarin rasuwar mukaddashin shugaban karamar hukumar Shira, Alhaji Adamu Wali. Marigayin ya rasu ne bayan jinya.
Masu zafi
Samu kari