Rashin Imani: Bam Ya Tashi da Mutane da Yawa, Yan Ta'adda Sun Bi Su da Harbi a Borno

Rashin Imani: Bam Ya Tashi da Mutane da Yawa, Yan Ta'adda Sun Bi Su da Harbi a Borno

  • Wani bam da ake zargin mayakan Boko Haram suka dasa, ya tashi da manoma, masu kamun kifi da masu zuwa yin itace a jihar Borno
  • Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa akalla mutane 20 sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka ji raunuka daban-daban
  • Wata majiya ta ce yawancin waɗanda abin ya shafa manoma ne da kuma masu zuwa yin itace da suka shiga daji domin shirin noma kafin zuwan damina

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno, Nigeria - 'Yan ta'adda da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne, sun sake tashin bam a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Akalla mutane 20 da suka hada da masu kamun kifi da masu sare itace sun mutu sakamakon tashin bam din da ya rutsa da su kusa da garin Gwoza da ke jihar Borno.

Kara karanta wannan

Mummunan iftila'i ya fada wa Amurka, gari guda ya rushe, an rufe sansanin sojoji

Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bam ya tashi da mutane a Borno

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa ba ya ga kashe akalla mutane 20, an tattaro cewa wasu da dama sun raunata sakamakon fashewar bam din da ake zargin 'yan Boko Haram sun dasa.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Alhamis, 23 ga watan Afrilu, 2027 a ƙauyen Hambagda.

Wannan kauye na daga cikin garuruwan da gwamnatin Borno ta sake maida mutane gidajensu bayan samun saukin hare-haren yan ta'adda.

Yadda lamarin ya faru a cikin daji

Wata majiya daga kungiyar Civilian JTF ta ce wasu daga cikin waɗanda suka mutu masu zuwa sarar itace ne da suka je neman itace domin tallafa wa iyalansu.

“Rana ce mai cike da baƙin ciki a gare mu a Gwoza. Mun rasa kusan mutane 20, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harbin bindiga.
"‘Yan ta’addan sun dasa bam a hanya, sannan bayan fashewar bam din, suka bude wuta kan fararen hula da ba su ji ba kuma ba su gani ba,” in ji majiyar.

Kara karanta wannan

An cafke sojan Amurka da ya je kama shugaban kasar Venezuela

Wata majiya ta ce yawancin waɗanda abin ya shafa manoma ne da kuma masu zuwa yin itace da suka shiga daji domin shirin noma kafin zuwan damina, cewar rahoton Daily Post.

An fara gano gawarwakin mutane

Haka kuma wani mazaunin yankin ya tabbatar da cewa an gano gawarwaki 18 zuwa yanzu a yankunan da ke kusa da Gwoza, yana mai gargadin cewa adadin na iya ƙaruwa saboda har yanzu akwai mutane da ba a gano ba.

Gwamna Zulum.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum yayin ganawa da jami'an gwamnati a Maiduguri Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Source: Twitter

Mazauna yankin sun ce maharan na yawo a yankin suna kai hare-hare lokaci zuwa lokaci, lamarin da ya sake tayar da hankula kan matsalar tsaro musamman a yankunan noma yayin da lokacin shuka ke karatowa.

Harin ya ƙara nuna irin barazanar da manoma da mazauna karkara ke fuskanta a yankunan da ke fama da matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani harin da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Sojojin sun kuma samu nasarar kashe wani babban kwamanda da aka bayyana sunansa da Abu Umar Bundi Munzir tare da wasu ‘yan ta'adda 24 a musayar wuta.

Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai a shiyyar Arewa maso Gabas, Manjo-Janar Abdulsalam Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262