Kisan Mai Martaba Sarki Ya Jawo Matsala, an Kona Mutane 3 da Ransu a Plateau
- Aƙalla mutane uku da ake zargi da hannu a kisan basarake a Langtang ta Arewa da ke jihar Plateau sun rasa ransu a hannun matasa
- Rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun kashe basaraken gargajiya Ponzhi Kwallak a gidansa, inda suka kwace babur da wayarsa
- Lamarin ya jefa al’umma cikin tashin hankali da jimami, yayin da aka ce wasu matasa sun yi kokarin mika waɗanda ake zargin ga jami’an tsaro kafin wasu su ci karfinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Langtang, Plateau - An shiga wani irin yanayi a jihar Plateau sakamakon hallaka wasu mutane uku kan zargin kisan basarake wanda ya tayar da hankulan mutane.
Majiyoyi suka ce aƙalla mutane uku da ake zargi da hannu a kisan wani basarake a Langtang ta Arewa sun mutu bayan fusatattun mutane sun kona su da wuta.

Source: Facebook
Plateau: Ana zargin matasa da kisan basarake
Rahoton Leadership ya ce mutanen suna da alaƙa da kisan marigayi Ponzhi Kwallak, basaraken ƙauyen Kwallak, wanda aka kashe a gidansa.
Majiyoyi sun nuna cewa maharan sun kai masa hari da daddare, inda suka harbe shi tare da kwace babur da wayarsa kafin su tsere.
An ce kisan ya jefa al’ummar yankin cikin jimami da tashin hankali mai tsanani wanda ya jawo baza jami'an tsaro a yankin da kewaye.
Sannan an ji mazauna yankin sun cafke mutanen uku yayin da suke kokarin sayar da babur ɗin da aka sace, kuma sun amsa laifin.

Source: Original
Yadda wasu matasa suka yi kokarin bin doka
Wasu matasa sun yi kokarin mika su ga jami’an tsaro domin a dauki mataki na doka kamar yadda aka sha jan hankulan mutane game da daukar doka a hannu.
Sai dai wasu ɓata-gari sun rinjayi matasan, suka kwace waɗanda ake zargin tare da kona su kusa da sakatariyar karamar hukumar.

Kara karanta wannan
Rashin imani: Bam ya tashi da mutane da yawa, yan ta'adda sun bi su da harbi a Borno
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce:
“Mazauna yankin ne suka kama waɗanda ake zargin, kuma an ce sun amsa laifin kafin fusatattun matasa su afka musu su kuma kona su.”
Majiyar ta ƙara da cewa an kai wa marigayin basaraken hari a gidansa, inda aka harbe shi tare da kwace babur da wayarsa kafin maharan su tsere.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro ba, kamar yadda rahoton Daily Post ya ce.
'Yan bindiga sun kashe basarake a Benue
A baya, an ji cewa 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Benue a tsakiyar Najeriya.
Tsagerun 'yan bindigan sun saje da mutane kafin daga bisani su kutsa fadar basarake tare da hallaka shi da iyalansa lamarin da ya tayar da hankulan al'umma.
'Yan bindigan sun kuma kashe karin wasu mutane a harin wanda suka kai a karamar hukumar Agatu ta jihar Benue da ke fama da matsalolin tsaro a yankin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
