Sanata Natasha Ta Fadi Matakin Dauka bayan Kotu Ta Umarci Ta Biya Diyyar N1bn

Sanata Natasha Ta Fadi Matakin Dauka bayan Kotu Ta Umarci Ta Biya Diyyar N1bn

  • Wata babbar kotu da ke zamanta a birnin Lokoja ta samu Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan da laifi a shari'arta da Yahaya Bello
  • Kotun ta umarci Sanata Natasha ta biya diyyar N1bn bayan ta same ta da laifi kan zargin bata sunan tsohon gwamnan na Kogi
  • Sanata Natasha ta bayyana matakin da za ta dauka kan hukuncin kotun wanda ta ce ko kadan ba ta yarda da shi ba

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi martani kan hukuncin da kotu ta yanke a shar'arta da Yahaya Bello.

Sanata Natasha ta yi watsi da hukuncin wamda wata babbar kotu da ke Lokoja ta yanke, inda ta umarci ta biya diyya.

Sanata Natasha za ta daukaka kara
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a ofishinta a majalisar dattawa Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Twitter

Sanata Natasha ta yi martani kan hukuncin kotun ne a wani bidiyo da ta sanya a shafinta na Facebook a ranar Juma'a, 24 ga watan Afirilun 2026.

Kara karanta wannan

Babban lauya ya hango haramci a shari'a da sojojin da suka shirya kifar da Tinubu

Kotun ta umarce ta da ta biya N1bn a matsayin diyya ga tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, kan kalaman ɓatanci.

Wane martani Sanata Natasha ta yi?

Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bayyana cewa za a ƙalubalanci hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.

Yayin da take mayar da martani kan hukuncin, Akpoti-Uduaghan ta ce kalaman da ta yi a gidan talabijin martani ne kai tsaye ga “munanan zarge-zargen” ta’addanci da tsohon gwamnan ya yi mata.

“Na fito a gidan talabijin ne domin ƙaryata zarge-zargen da aka yi mini. An jefe ni da laifin ta’addanci, kuma ina da cikakken haƙƙin kare kaina a gaban al’ummar Najeriya."
“Idan har akwai wanda za a zarga da ta’addanci, to ya kamata ya zama Yahaya Bello ne, ba ni ba.”

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Natasha ta yi watsi da hukuncin kotu

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ƙara da cewa kotun ta kasa yin la’akari da kwararan hujjojin da ta gabatar domin goyon bayan iƙirarin nata.

“Na yi watsi da wannan hukuncin gaba ɗaya. Mun gabatar da isassun hujjoji a gaban kotu domin kare matsayinmu, amma a bayyane yake cewa ba a tantance su yadda ya kamata ba.”

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci a shari'ar Sanata Natasha da Yahaya Bello, ta umarci biyan N1bn

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Ta jawo hankali kan yanayin tsaro a jihar Kogi a lokacin mulkin Yahaya Bello, inda ta yi zargin cewa iyalai da dama har yanzu suna cikin makoki sakamakon asarar da suka yi a wannan lokacin.

“An tafka kisan-ƙiyashi da dama a jihar Kogi, musamman a yankin Kogi ta Tsakiya, lokacin da yake gwamna."
“Iyalai da dama sun ci gaba da kuka kullum kan rashin masoyansu. Waɗannan lamura ne na gaske waɗanda ba za a iya yin watsi da su ba.”

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Natasha ta kare kanta

Sanatar ta nanata cewa kalaman nata an yi su ne don neman gaskiya da riƙon amana, tana mai jaddada cewa tana nufin jawo hankali ne ga halin da al’ummomin da abin ya shafa ke ciki.

Sanata Natasha ta yi watsi da hukuncin kotu
Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook
“Kalamaina sun samo asali ne daga abubuwan da mutanenmu suka fuskanta da kuma buƙatar faɗar gaskiya ga masu iko."
“Wannan maganar ba ta ƙare a nan ba. Za mu nemi haƙƙinmu a kotun ɗaukaka ƙara domin tabbatar da cewa adalci ya yi tasiri.”

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: EFCC ta gabatar da shaida a shari'ar tsohon gwamnan Kogi

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata Natasha ta tada rigima a majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi musayar yawu da shugaban kwamitin ma'adanai da karafa na majalisar dattawa, Patrick Ndubueze.

Lamarin ya faru ne yayin tattaunawa a zaman da kwamitin ya shirya domin kare kasafin kudi ma’aikatar raya masana’antar karafa.

Shugaban kwamitin ya dakatar da Natasha lokacin da take gabatar da tambayoyinta wanda hakan ya sanya ta yi masa martani mai zafi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng