Gaza: Batun Falasdinu da Abubuwan da Fafaroma Leo XIV Ya Tabo yayin Fara Huduba
Sabon Fafaroma da aka nada, Leo XIV ya fara jawabin Lahadi na farko da kira da a kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe a duniya.
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Rome - Sabon Fafaroma da aka nada a makon da ya wuce, Leo XIV ya yi hudubar Lahadi ta farko a fadar Vatican.
Fafaroma Leo XIV ya nuna damuwarsa kan rikicin Ukraine da yaƙin Isra’ila da Hamas a Gaza, yana roƙon zaman lafiya na gaskiya mai dorewa.

Asali: Getty Images
A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu muhimman abubuwa da sabon Fafaroman ya yi ga mabiya addinin Kirista.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Kira da zaman lafiya a Ukraine da Gaza
Fafaroma Leo XIV ya yi kira na musamman kan samun zaman lafiya na gaskiya mai dorewa a Ukraine, inda rikici tsakanin Rasha da Ukraine ya jima yana cigaba.
Ya ce ya damu matuƙa da yadda abubuwa ke faruwa a Zirin Gaza, inda Isra’ila da Hamas ke fafata wa cikin rikicin da ya lakume rayuka da dama.

Asali: Facebook
RFI ta rahoto cewa Fafaroma Leo XIV ya ce:
“Ya kamata a nuna jin ƙai ga fararen hula da suka gaji da wannan yaƙin, kuma a sako dukkanin waɗanda aka yi garkuwa da su,”
Yaƙin da ake yi a Gaza a yanzu, wanda ya fara a watan Oktoban 2023, ya zama na 15 cikin jerin rikice-rikicen Falasdinawa da Isra’ila tun farko.
Fafaroma Leo ya bukaci duka ɓangarorin da su nemi mafita ta hanyar sulhu da nuna tausayi da jin ƙai, ba farmaki ba.
2. Girmamawa ga marigayi Fafaroma Francis
Leo XIV ya bayyana cewa zai ci gaba da bin tafarkin marigayi Fafaroma Francis wanda ya rasu a watan Afrilu yana da shekara 88.
Ya ce Fafaroma Francis ya bar kyakkyawan misali na tsayin daka wajen hidimar mutane da rayuwar da ke da sauƙi.

Asali: Getty Images
A ranar Asabar, Leo ya ziyarci kabarin Francis da ke cocin Santa Maria Maggiore, inda ya yi addu’a a can cikin tawali’u da nutsuwa.
Wurin ne cocin da Fafaroma Francis ya fi so, kuma har yanzu mabiya na ci gaba da ziyarar kabarinsa.
3. Fadin cewa Fafaroma bawan Allah ne
Leo ya bayyana kansa a matsayin “bawa mai tawali’u” kuma bai cancanci rike babban matsayin da aka ba shi ba.

Asali: Twitter
Sabon Fafaroman ya yi magana yana mai cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen hidimar ɗaukacin mabiya cocin Katolika da duniya baki ɗaya.
4. Shirin ayyuka da ganawa da duniya
Bayan kammala hudubar farko ta ranar Lahadi, fadar Vatican ta fitar da jadawalin ayyukan da Fafaroma Leo zai fara.
A yau Litinin Fafaroma Leo zai gana da wakilan kafofin watsa labarai daga sassa daban-daban na duniya.

Asali: Getty Images
Baya ga haka, sabon Fafaroman ya shirya ganawa da jakadun ƙasashen duniya a Vatican a ranar Juma’a.
Rahoton Vatican News ya nuna cewa a ranar Lahadi 18 ga Mayu, Leo zai jagoranci babban taron addu’a.
Bayan wannan, a ranar 21 ga Mayu, zai fara taron mako-mako inda zai rika karatu da kuma gabatar da wa’azi.
Fafaroma Leo zai fuskanci kalubalen hada kan cocin Katolika da kuma samar da zaman lafiya a duniya, kuma tuni mabiya da dama sun nuna goyon bayansu ga jagorancinsa.
Shin wanene Fafaroma Leo XVI?
A wani rahoton, kun ji cewa an bayyana wasu muhimman abubuwa game da sabon Fafaroma da aka nada a Vatican.
Daga cikin abubuwan da aka ambata game da Fafaroman Leo shi ne kasancewarsa na farko a cikin wadanda suka rike mukamin daga Amurka.
Legit ta rahoto cewa Fafaroman yana jin yaruka da dama wanda ana ganin hakan zai tamaka masa wajen sauke nauyin da aka daura masa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng