Kwankwaso Ya Ƙara Tono Rigima, Tsagin NNPP Ya Kira Shi da 'Maci Amana'

Kwankwaso Ya Ƙara Tono Rigima, Tsagin NNPP Ya Kira Shi da 'Maci Amana'

  • Kalaman jagoran NNPP na ƙasa, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso sun harzuƙa tsagin jam'iyyar ƙarƙashin jagorancin Major Agbo
  • Tsagin Agbo ya caccaki Kwankwaso bisa kiran wasu ƴan NNPP da suka koma jam'iyyar APC da ci maciya amana na ƙarshe
  • Agbor ya bayyana Kwankwaso da maci amana na gaske, wanda daga ba shi mafaka a zaɓen 2023 yana neman kwace iko da NNPP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Tsagin jam’iyyar NNPP karkashin jagoranci Major Agbo ya maida martani mai zafi ga tsohon dan takarar shugaban kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Tsagin NNPP ya soki Kwankwaso ne bisa kalaman da ya yi kan ƴaƴan jam'iyyar da suka sauya sheka zuwa APC mai mulki.

Madugun Kwankwasiyya.
Tsagin NNPP ya sake dura kan Kwankwaso, ya ce shi ne asalin maci amana Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

NNPP ta yi fatali da kalaman, tana mai cewa babu wani maci amana na ƙarshe kamar Kwankwaso, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman Kwankwaso sun tono rigima

Tun farko dai jagoran NNPN na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya kira waɗanda suka sauya sheka zuwa APC a matsayin maciya amana na karshe.

A cewarsa, yadda talakawa suka haƙura da taliya da atamfar da ƴan siyasa suka raba a Kano a 2023, suka fito suka zaɓe su kaɗai ya isa hujjar cewa abin da suka yi cin amana ne.

Madugun Kwankwasiyya ya yi wannan furucin ne da ya karɓi baƙuncin ƴan Kwankwasiyya daga ƙaramar hukumar Takai a gidansa da ke Kano.

Sai dai a wata sanarwa da shugaban tsagin NNPP na kasa, Dr. Agbo Major, ya fitar a yau Litinin a Legas, jam’iyyar ta ce:

“Kwankwaso ba shi da ikon magana a madadin NNPP domin an kore shi tun bayan zaben 2023 tare da wasu daga cikin magoya bayansa da suka shigo jam’iyyar.”
Agbo Major.
Major Agbo ya ce Kwankwaso ne asalin wanda ya ci amanar NNPP Hoto: Major Agbo
Asali: Twitter

“Kwankwasiyya ba jam’iyya ba ce” – NNPP

A rahoton Punch, Major ya kara da cewa:

“Kwankwasiyya wata kungiya ce da aka amince da ita a matsayin wani bangaren yakin neman zabe na Kwankwaso a 2023, amma ba jam’iyya ba ce.”
"Abin dariya ne Kwankwaso ya fito yana zargin wasu da cin amana, alhali shi ne ya nemi mallake NNPP da karfi, bayan mun ba shi takarar shugaban kasa kyauta, shi ne asalin maci amana."
“Duka ‘yan Najeriya na da yancin sauya sheka zuwa kowace jam’iyya da suke so. Kwankwaso ba zai hana ‘ya’yansa komawa APC ko wata jam’iyyar ba.”

Major ya ce yanzu Kwankwaso ya rasa ƙarfinsa a Kwankwasiyya, ya kuma ƙalubalance shi da ya je ya kirkiro sabuwar jam’iyya ko ya shiga wata daban.

Jam'iyyar NNPP ta ƙara karfi a Kano

Kuna da labarin cewa, jagoran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya karɓi masu sauya sheƙa sama da 150 daga APC a karamar hukumar Takai ta jihar Kano.

Masu sauya shekar sun bayyana sun yanke shawarar raba gari da APC ne saboda rashin shugabanci nagari, wanda al'umma ke fatan samu.

Ana ganin hakan ya ƙara tabbatar da yadda NNPP ke ƙara samun karɓuwa musamman saboda manufa da tsarin da gwamnatin Kano ke tafiya a kai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262