Bayan Kalaman Kwankwaso, Dan Majalisar NNPP Ya Sauya Sheka zuwa NNPP a Kano
- Jam'iyyar NNPP mai mulki da rinjaye a jihar Kano ta samu naƙasu a majalisar dokokin jihar bayan ficewar ɗaya daga cikin mambobinta
- Hon. Zubairu Hamza Masu mai wakiltar mazaɓar Sumaila a majalisar dokokin ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC mai adawa a jihar Kano
- Ɗan majalisar ya nuna cewa rikicin cikin gida da ya addabi NNPP na daga cikin dalilan da suka sanya ya tattara ƴan komatsansa ya bi APC
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Wani ɗan majalisar dokoki ta jihar Kano mai wakiltar mazaɓar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Hon. Zubairu Hamza Masu ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC bayan ya fice daga NNPP mai mulki a Kano.

Asali: Facebook
Ɗan majalisar ya sanar da ficewarsa daga NNPP ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Rt. Hon. Ismail Falgore, cewar rahpton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ɗan majalisar NNPP ya fice a Kano?
Hon. Zubairu Hamza Masu ya bayyana cewa rikicin ɓangaranci da shari’un da suka addabi NNPP ne babban dalilinsa na barin jam’iyyar.
Shugaban majalisar ya karanta wasiƙar a zauren majalisar yayin zaman ta na ranar Litinin, inda ya bayyana cewa murabus ɗin Hon. Zubairu Hamza Masu daga NNPP ya fara aiki daga ranar 12 ga watan Mayu, 2025.
Hon. Zubairu Hamza Masu ya kuma bayyana cikakkiyar biyayyarsa ga shugabancin APC daga matakin mazaɓa har zuwa ƙasa baki ɗaya.
Ɗan majalisar ya ƙara da cewa mutane da dama daga matakin jiha da ƙasa suna rikici da juna kan shugabancin jam’iyyar NNPP.
Rikicin gida ya raba kan jam'iyyar NNPP
Ya ambaci Dr. Suleiman Hashim Dungurawa da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa a matsayin masu iƙirarin shugabancin NNPP a matakin jiha.
Hakazalika ya ce Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major na iƙirarin shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa, lamarin da ya jefa jam’iyyar cikin rikicin shari’a.

Asali: Facebook
Zubairu Hamza Masu ya bar tafiyar Kwankwasiyya
Tun a kwanakin baya ne dai ɗan majalisar ya sanar da ficewarsa daga tafiyar Kwankwasiyya amma ya ci gaba da zama a cikin jam'iyyar NNPP.
A lokacin ya bayyana cewa ya fice daga tafiyar Kwankwasiyya ne saboda abin da ya kira rashin karɓar shawararsu da ake yi idan suka ba da.
Ficewarsa na zuwa ne bayan Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC.
Kwankwaso ya tarbi ƴan APC zuwa NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban jigo a jam'iyyar NNPP kuma madugun tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya tarbi masu sauya sheƙa daga APC.
Rabiu Musa Kwankwaso ya tarbi tsofaffin mambobin na APC ne guda 170 da suka sauya sheƙa zuwa jam!iyyar NNPP waɗanda suka fito daga ƙaramar hukumar Takai.
Jagoran na NNPP ya yabawa tsofaffin mambobin na APC bisa jajircewar da suka nuna, inda ya ce dama jam'iyyar NNPP an samar da ita ne don amfanin talaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng