Sabon Rikici Ya Barke a Jami'ar Katsina, Ana Zargin 'VC' da Aikata ba Daidai ba
- Rikicin shugabanci ya sake ɓarkewa a FUDMA bayan zaɓen sabon shugaban jami'ar, inda 'yan takara suka soki yadda aka gudanar da zaɓen
- Wasu 'yan takara sun zargi shugaban jami'ar mai barin gado da amfani da matsayinsa don ganin ɗan takarar da yake so ya samu nasara
- Farfesa Sadiq Radda ya shigar da ƙara ga ministan ilimi kan zargin cire shi ba bisa ƙa'ida ba, yayin da Farfesa Usman Dustinma ya ce an nuna son kai
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Rikicin shugabanci ya sake mamaye jami’ar tarayya da ke Dutsin-Ma (FUDMA), a jihar Katsina, biyo bayan gudanar da zaɓen sabon shugaban shugaban jami’ar.
Rikicin ya ɓarke ne bayan da majalisar gudanarwar jami’ar ta zaɓi ‘yan takarar da suka tsallake matakin tantance ta farko, a neman mukamin shugaban jami’ar (VC).

Asali: Twitter
Rikicin shugabanci ya barke a jami'ar Katsina
Wasu daga cikin waɗanda suka nemi wannan matsayin, kuma suke ganin ba a yi masu adalci ba, sun soki yadda aka gudanar da zaɓen, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan takarar sun zargi shugaban jami’ar mai barin gado, Farfesa Armayau Bichi, da yin amfani da matsayinsa wajen ganin cewa ɗan takarar da yake so shi ya samu nasara.
Waɗannan zarge-zargen sun jawo hankalin mutane, musamman da wasu ‘yan takara biyu suka shigar da ƙararraki domin kalubalantar yadda aka gudanar da zaɓen.
Sai dai Farfesa Bichi ya musanta zarge-zargen, inda ya ce an gudanar da zaɓen ne cikin tsari na gaskiya da kuma adalci.
Ƙararraki kan shugaban jami’a mai barin gado
Ɗaya daga cikin ‘yan takarar, Farfesa Sadiq Radda, ya shigar da ƙara ga ministan ilimi, Tunji Alausa, inda ya zargi wani shiri da aka yi na ɓata zaɓen da kuma ganin cewa an cire shi daga cikin waɗanda suka cancanta.
Farfesa Radda, wanda farfesa ne a sashen nazarin kungiyoyin jama’a a jami’ar Bayero da ke Kano, ya yi iƙirarin cewa an cire wasu ‘yan takara da suka cancanta.
Ya ce masu tantancewar ba su bayar wani dalili mai gamsarwa ba duk da cewa wadanda aka cire sun cika dukkanin ƙa’idojin da aka bayyana a tallar neman aikin.
Ya zargi shugaban jami’ar, Bichi (mai barin gado) da ƙoƙarin ganin cewa an naɗa wani ɗan takara wanda bai kai sauran cancanta ba.

Asali: Facebook
Farfesa Dutsinma ya yi zargin an nuna son kai
Wani ɗan takarar matsayin shugaban jami’ar, Farfesa Usman Aliyu Dustinma, ya shigar da ƙara ga majalisar gudanarwar jami’ar, ya zargi nuna son kai, rashin bin ƙa’ida, da kuma rashin gaskiya a cikin zaɓen da ake yi.
A cikin wasiƙarsa mai kwanan watan 28 ga Afrilu, 2025, wadda aka kuma aika irin ta ga ministan ilimi, Tunji Alausa, Farfesa Dustinma ya soki yadda ake gudanar da zaɓen, ya yi iƙirarin cewa an yi watsi da cancanta da kuma bin doka don fifita wasu ‘yan takara da ake so.
Ya zargi cewa an karkatar da zaɓen don amfanar wani ɗan takara na musamman, sabanin ƙa’idojin da aka tallata da kuma hanyoyin da suka dace wajen naɗa shugabannin jami’o’in tarayya a Najeriya.
Dukkan ‘yan takarar biyu da suka shigar da korafinsu, sun nuna gamsuwarsu da kokarin da gwamnatin tarayya ta nuna wajen shiga tsakani a lamarin.
Farfesa Radda da Farfesa Dustinma sun yi kira ga ministan ilimi da ya sake duba dukkanin zaɓen don tabbatar da adalci da kuma kare martabar jami'ar.
'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar FUDMA
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai biyu na jami'ar tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA) a jihar Katsina.
Maharan sun shiga unguwar Graveyard Quarters da ke kan hanyar Tsaskiya a garin Dutsin-Ma da misalin ƙarfe 2:40 na dare, suka yi awon gaba da ɗaliban.
Bayan samun kiran gaggawa, jami'an tsaro sun kai ɗauki cikin gaggawa don hana 'yan bindigan tserewa tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng