"Babu Bambanci," Gwamna Ya Girgiza Siyasar Najeriya, Ya Ce APC da PDP Manufarsu 1

"Babu Bambanci," Gwamna Ya Girgiza Siyasar Najeriya, Ya Ce APC da PDP Manufarsu 1

  • Mai girma Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya yi ikirarin cewa duka jam'iyyun siyasa a Najeriya manufarsu guda
  • Wannan kalamai da gwamnan ya yi na zuwa ne a daidai lokacin da jita-jita ke ƙara ƙarfi cewa yana shirin sauya sheka daga PDP zuwa APC
  • Eno ya ce jam'iyyun siyasa tsani ne kawai da ake takawa domin a ci zaɓe amma bayan mutum ya yi nasara, zai zama shugaba ga kowa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Yayin da jita-jita ke kara yaduwa cewa yana shirin sauya sheka zuwa APC mai mulki, Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Pastor Umo Eno, ya ce duka jam'iyyun siyasa manufarsu ɗaya.

Gwamna Umo Eno ya yi ikirarin cewa da APC da PDP duk abu guda ne domin manufarsu ɗaya a siyasar Najeriya.

Gwamna Umo Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya kata nuna alamun yana shirin canza sheka daga PDP zuwa APC Hoto: Fastor Umo Eno
Asali: Twitter

Mai girma gwamnan ya yi wannan furucin ne a wurin wani taro da aka gudanar a ƙaramar hukumar Itu/Ibiono ranar Alhamis da ta shuɗe, Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya ƙalubalanci ƴan Najeriya

A jawabin da ya yi a wurin taron, gwamnan ya kalubalanci duk ɗan Najeriya da ke ganin ɓa haka bane da ya nuna masa banbancin manufofin jam’iyyun siyasar kasar nan.

Gwamna Eno ya ce:

“Ban ga inda PDP da APC suka sha bamban ba. In akwai wanda ke ganin na yi kuskure ya fito nan ya gyara mani.
"Ina wannan magana ne a gaban talabijin na kasa wanda kowa zai iya gani, a zo a nuna min bambancin akidar siyasa tsakanin PDP, APC da YPP.”

APC da PDP ba su da banbanci a siyasa

Gwamnan ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa “tamkar ababen hawa ne zuwa ga wata manufa”, inda ya ce idan mutum ya ci zabe, to gaba ɗaya al’umma zai mulka.

Duk da Gwamna Eno ya hau mulki ne a ƙarƙashin PDP a 2023, amma an ga yana ɗasawa da manyan jiga-jigan APC a jihar Akwa Ibom da kasa baki ɗaya.

Alamu sun nuna akwai kyakkywar fahimta da haɗin kai tsakanin Gwamna Eno da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda tsohon gwamna ne a Akwa Ibom.

Gwamna Umo Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya nuna alamun zai bar PDP zuwa APC Hoto: Fastor Umo Eno
Asali: Facebook

Ana ƙishin-ƙishin Gwamna Eno zai koma APC

Gwamnan ya fito fili ya bayyana goyon bayansa ga shugabancin Bola Tinubu da Sanata Akpabio, yana mai cewa yana son tsohon gwamnan ya zarce a kujerar shugaban Majalisar Dattawa.

Haka nan kuma Akpabio ya maida biki, inda shi ma ya fito ya ayyana goyon bayansa ga Gwamna Eno, yana mai cewa ya cancanci tazarce a zaɓen 2027.

Wannan da ma wasu dalilai na cikin abubuwan da ake ganin Gwamna Eno na shirin tattara kayansa ya bar PDP zuwa APC, in ji rahoton Leadership.

PDP ta fara rarrashin Gwamnan Akwa Ibom

A baya, kun ji cewa jam'iyar PDP ta nuna damuwa game da yiwuwar sauya shekar gwamnan Akwa Ibom watau Fasto Umo Eno.

PDP ta soki matakin da Gwamna Eno ke shirin ɗauka na komawa APC, tana mai cewa bai kamata ya yi wa jam'iyyar da ta ba shi matsuguni tsawon shekaru butulci ba.

Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya ce kamata ya yi gwamnan ya tsaya a PDP domin kare tsari da demokuradiyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262