Minista Ya Take Umarnin Tinubu, Ya Yi Murabus daga Mukaminsa? An Samu Bayani

Minista Ya Take Umarnin Tinubu, Ya Yi Murabus daga Mukaminsa? An Samu Bayani

  • Tsohon ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya musanta rahotanni da ake yadawa cewa ya yi murabus ba tare da izinin Bola Tinubu ba
  • Daya daga cikin hadimansa, Femi Awogboro ya ce sai da Shugaba Bola Tinubu ya amince kuma ya sa albarka kafin Adelabu da ajiye aiki
  • Ya jaddada cewa tsohon ministan zai maida hankali wajen neman takarar gwamnan Oyo a zaben 2027, domin ci gaba da hidimata wa al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - An karyata rahotannin da ke cewa tsohon Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya yi murabus ba tare da amincewar Shugaba Bola Tinubu ba.

Daya daga cikin hadimansa, Femi Awogboro, ya bayyana cewa Adelabu ya samu cikakkiyar amincewa da albarkar shugaban kasa kafin ya yanke shawarar sauka daga mukaminsa.

Adelabu.
Tsohon Ministan lantarki, Adebayo Adelabu yana magana da yan jarida kan ayyukansa a Abuja Hoto: Adebayo Adelabu
Source: Twitter

A cewarsa, rahotannin da ke cewa an yi hakan ba tare da yardar shugaban kasa ba, ba su da tushe balle makama, kamar yadda Tribune Nigeria ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda minista ya yi murabus duk da Shugaba Tinubu bai so hakan ba

Dalilin murabus din Ministan Lantarki

Awogboro ya ce baya ga burinsa na tsayawa takarar gwamna, Adelabu ya taba nuna irin wannan sadaukarwa a baya lokacin da ya yi murabus daga mukamin Mataimakin Gwamna a Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ya kara da cewa Adelabu mutum ne da ke yanke hukunci bayan ya nemi zabin Ubangiji da kuma neman shawarar mahaifinsa da ta jagoransa, Shugaba Tinubu.

Awogboro ya bukaci masu yada bayanan karya su daina, yana mai cewa masu sukar Adelabu ba su da wani hujja face hassada da dimuwar da suka samu daga irin tarbar da aka yi masa a Ibadan.

Abin da ya sa Adelabu zai nemi takara

Ya ce al’ummar jihar Oyo ne ke kira ga Adelabu da ya jagorance su, tare da nuni da irin kwarewarsa da kuma kusancinsa da talakawa.

A cewarsa, goyon bayan da uban gidansa ke samu ya fito fili a ranar Alhamis 23 ga Afrilu, lokacin da ya isa filin jirgin sama na Alakia a Ibadan, inda dubban mutane daga kananan hukumomi 33 na jihar suka fito tarbarsa.

Kara karanta wannan

Cin bashi: Fadar shugaban kasa ta yi wa Sanusi II martani kan sukar Tinubu

Adelabu.
Tsohon ministan lantarki, Adebayo Adelabu lokacin da ya ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Awogboro ya jaddada cewa murabus din bai saba wa ra’ayin Shugaba Tinubu, illa dai an yi shi ne da cikakkiyar yardarsa domin ba shi damar ci gaba da hidima ga al’umma ta wata hanya daban.

Ya jaddada cewa tsohon ministan zai maida hankali wajen neman takarar gwamnan jihar Oyo a zaben 2027, domin ci gaba da hidimata wa al'ummar da ke nuna masa kauna, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Tinubu ya rantsar da sabon ministan gidaje

A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Dr. Muttaqha Rabe Darma a matsayin Ministan gidaje da raya birane a fadar shugaban ƙasa, Abuja.

Taron rantsuwar ya gudana ne a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Juma'a, 24 ga Afrilu, 2026.

Shugaba Tinubu, a cikin takaitaccen bayani da ya yi yayin taron rantsuwar, ya taya Dr. Darma murna tare da bayyana shi a matsayin gwani a harkar gidaje.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262