Latest
A yayin da Hausawa kan ce dan Kuka da bai ji ba kuma bai gani ba ya ke janyowa Uwar sa duka, hakan kuwa ta kasance ga wata Mata da dan da ta haifa ya yi ma ta zundur ta hanyar yaye ma ta zani a gaban Kotu wajen tonan makircin ta.
Gwamnatin tarayya ta saki kudade domin sayan jiragen yaki kirar "Tucano" 12 daga kasar Amurka domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya. Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal S.B Abubakar.
An bukaci daukacin al'ummar musulmai da su kauracewa wata takardar goge najasa kamar su kashi ta M&S sakamakon wani rubutu dake ishara da sunan Allah dake a saman ta da larabci kamar dai yadda wasu 'yan uwa suka bankado. Labarin t
A yau Litinin, jagoran mabiya addinin Kirista 'yan akidar Katolika na duniya, Jorge Mario Bergoglio da aka fi sani da Fafaroma, yayi karin haske kan hukuncin jin kai da ya cancanci Matan da suka zubar da jiki a madadin hukunta su.
Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC, ta tantance wasu kungiyoyi 116 na Najeriya da kuma na kasa-da-kasa 28 da za su sanya idanun lura akan babban zaben kasa da zai gudana cikin fadin Najeriya a watan gobe da jibi.
Uwargidar tsohon mataimakin Shugaban kasa, Amina Namadi-Sambo ta koka kan yadda akee tozarta matan Musulmi da ke sanya hiabi a wasu yankunan kasar, cewa hakan ya take hakkin yancin mata na yi kowace irin addini.
Za ku ji ko su wanene su kayi fice wajen bada kyautar dukiyar su. Mun tsakuro wannan jeri na a wani tsohon rubutu da The Thrive Global tayi. Daga cikin masu taimako akwai Bill and Melinda Gates Foundation mai agazawa marasa karfi.
Mukaddashin sifeton yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya nada sabbin mataimakan sifeton yan sanda shida a ranan Litinin, 28 ga watan Junairu, 2018. Premium Times ta bada rahoto. Sabbin jami'an yan sandan ya aka karawa matsayi
Jihar Bauchi da ke yankin arewacin Najeriya na gab da zama tamkar jihohin Niger Delta masu arzikin man fetur. Gwamnatin tarayya na ci gaba da aikin hako rijiyoyin mai a kauyen Kolmari da ke karamar hukumar Alkaler na jihar.
Masu zafi
Samu kari