Gulbi: Attajiran Duniya da ke da yawon kyauta na kin-karawa

Gulbi: Attajiran Duniya da ke da yawon kyauta na kin-karawa

Mun shiga zauren Attajiran Duniya wanda su kayi fice wajen sakin hanu da bada kyautar dukiyar su kamar ba su da bukata. Mun tsakuro wannan jeri na a wani tsohon rubutu daga wani shafi na kasar waje mai suna The Thrive Global.

Gulbi: Attajiran Duniya da ke da yawon kyauta na kin-karawa
Bill Gates yana cikin wadanda su ka fi kowa kyata
Asali: Depositphotos

Ga dai sunayen wadannan Bayin Allah nan kamar yadda aka taba kawo sunayen su a bara:

1. Bill Gates

Bill Gates wanda ba bako bane cikin Attajiran da ake ji da su a Duniya, ya cire sama da Dala biliyan 27 daga cikin dukiyar sa ya bada kyauta daga lokacin da yayi kudi zuwa yanzu. Gidauniyar sa kan taimakawa Yara a fadin Duniya.

2. Warren Buffett

Akalla ba a kasara, Warren Buffet ya batar da abin da ya haura Dal biliyan 21 na kudin sa wajen taimakon ,marasa karfi. Buffet ya hada kai ne gidauniyar takwaran sa watau Bill and Melinda Gates Foundation wajen taimakawa jama’a.

3. George Soros

George Soros asali mutumin kasar Hungary ne wanda yanzu ya tare a Amurka, ya kuma yi kaurin suna wajen taimakon marasa hali. Soros ya kashe fiye da Dala biliyan 8 wajen inganta harkar lafiya da kuma bangaren siyasa da zaman lafiya.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya tayi karin haske game da karin albashi

4. Azim Premji

Attajirin nan Azim Premji na kasar Indiya ya kashe kudi shi ma akalla Dala biliyan 8 wajen taimakon marasa karfi yanzu haka. Premji ya biyewa Buffet wajen ganin sun yi amfani da dukiyar su domin al’umma su amfana da baiwar ta su.

5. Charles F. Feeney

Ana yi wa Charles Feeney da lakabi da sunan wani ‘dan wasan kwaikwayo mai suna James Bond. An sa Feeny wannan suna ne saboda irin taimakon da yake badawa ba tare da kowa ya sani ba. Feeny ya batar da kusan duk kudin sa wajen kyauta.

Sauran wadanda su kayi kaurin-suna wajen rashin kyashin bada kudi a Duniya sun hada da Carlos Slim, da wani sanannen Balarabe mai suna Sulaiman bin Abdulaziz Al Rajhi, da irin su Gordon Moore, Michael Bloomberg da kuma Mark Zuckerberg.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel