Da duminsa: Daga sallamar manyansa, IGP Adamu ya karawa AIG's 6 matsayi

Da duminsa: Daga sallamar manyansa, IGP Adamu ya karawa AIG's 6 matsayi

Mukaddashin sifeton yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya nada sabbin mataimakan sifeton yan sanda shida a ranan Litinin, 28 ga watan Junairu, 2018. Premium Times ta bada rahoto.

Sabbin jami'an yan sandan ya aka karawa matsayi zuwa mukamin DIG sune Usman Tilli Abubakar, daga jihar Kebbi wanda ya shiga hukumar a shekarar 1986; AbdulMajid Ali, daga jihar Neja wanda ya shiga aikin yan sandan shekarar 1986; Taiwo Frederick Lakanu, daga jihar Legas ya shiga hukumar a shekarar 1986; da Godwin Nwobodo, daga Enugu kuma ashiga hukumar shekarar 1984.

Sauran jami'an yan sandan da aka karawa girma daga matsayin kwamishana CP zuwa DIG sune, Ogbizi Michael, tsohon kwmaishanan yan sandan jihar Abiya da Ibrahim Lamorde, tsohon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

An bayyana wannan karin girman ne da safiyar Litinin kuma an tura sunayensu ofishin lura da ayyukan hukumar yan sanda.

KU KARANTA: Mukaddashin CJN, Tanko Muhammed, ya jagoranci zaman kotun koli

Wannan abin ya faru ne kwana daya bayan Sifeto Janar na sandan, Adamu Mohammed, ya yiwa dukkan manyan jami'an yan sandan da suka girmeshi a makami ritaya.

Mataimakan Sifeta Janar na rundunar da ritayar ta shafa sun ahada da Maigari Dikko, da ke kula da sashen kudi da mulki da kuma Habila Joshak, da ke kula da ayyuka.

Sauran biyar din sun hada da Emmanuel Inyang, mai kula da sashen watsa labarai da sadarwa; Agboola Oshodi-Glover, sashen shigo da kaya da dabaru; Mohammed Katsina, sashen bincike da tsare tsare; Sani Mohammed, sashen bunkasa horo ga jami'ai; da kuma Peace Ibekwe-Abdallah, sashen kwararru kan binciken laifukan ta'addanci na gwamnatin tarayya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel