Kaico! Yan bindiga dadi sun bindige Fulani makiyaya 2 a Katsina, sun yi awon gaba da yaro

Kaico! Yan bindiga dadi sun bindige Fulani makiyaya 2 a Katsina, sun yi awon gaba da yaro

Wasu mutane biyu sun gamu da ajalinsu a hannun wasu gungun yan bindiga da suka kai musu hari a kauyen Lungu dake garin Dan Ali, cikin karamar hukumar Danmusa ta jahar Katsina, sa’annan suka yi awon gaba da karamin yaro.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen wadanda aka kashe kamar haka; Rabiu Aikau da wani dan uwansu da ake kira Manya, sai kuma karamin yaron da yan bindigan suka yi garkuwa da shi, wanda rahotanni suka bayyana cewa yaron Aikau ne.

KU KARANTA: Zaben Ekiti: Kotu ta kunyata Fayose, ta tabbatar da nasarar gwamna Fayemi

Sai dai rahotanni sun kara da cewa mutanen biyu sun mutu ne a sakamakon tirjiya da suka nuna ma yan bindigan yayin da suka yi kokarin kwashe musu dabbobin da suke kiwatawa, tare da kuma yin awon gaba da yaronsu.

Amma fa duk kokarin da majiyarmu tayi na jin ta bakin rundunar Yansandan jahar Katsina game da wannan lamari ya ci tura, sai dai rundunar ta sanar da cewar a ranar 1 da 22 ga watan Janairu ta samu nasarar ceto wasu mutane biyu daga hannun masu garkuwa da mutane.

Kaakakin rundunar, ASP Gambo Isah ne ya sanar da haka a garin Katsina, inda yace sun ceto mutanen ne daga sansanin barayin mutane dake cikin karamar hukumar Dan Musa, inda ya bayyana sunayensu kamar haka; Aminu Lawal Chaji da Fatima Alhaji Haruna.

Kaakaki Gambo yace sun kwato bindigu guda biyu kirar AK-47 daga hannun yan bindigan, sauran abubuwan da suka kwato daga hannunsu sun hada da alburusai guda goma sha biyu samfuri daban daban.

Har ila yau rundunar Yansandan jahar Katsina ta bayyana cewa ta kwace bindigar AK 47 guda daya, alburusai da dama da kuma babura guda biyu kiran Bajaj daga hannun wasu miyagu bayan musayar wuta a jahar Katsina.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel