Yakin Boko Haram: Gwamnati ta saki kudin sayan jirage yaki kiran "Tucano" 12

Yakin Boko Haram: Gwamnati ta saki kudin sayan jirage yaki kiran "Tucano" 12

Gwamnatin tarayya ta saki kudade domin sayan jiragen yaki kirar "Tucano" 12 daga kasar Amurka domin yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Babban hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshal S.B Abubakar, ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai a ranan Lahadi, 27 ga watan Junairu, 2019.

Ya bayyana cewa hukumar sojin Najeriya na bukatar masu hannu da shuni wajen taimakawa siyan makamai musamman hadasu da kuma jirgin leken asiri.

Yace: "A shekaru uku da suka gabata, jiragen hukumar sojin sama sun samu cigaba matuka. A siya sabbin jirage 16, kuma an tayar da wasu 13 da suk lalace kuma ana kan gyara guda biyu."

"Kana, hukumar sojin sama na duba jiragen Aplha Jet 3 dake Kainji, a kuma jirgin L-39ZA guda uku dake jihar Kano."

"Sabbin jiragen da aka saya a shekarar 2018 sune 'Super Mushskhak' daga kasar Pakistan, sai jirgi mai saukar angulu kirar Mi-35M daga kasar Rasha, jirgi mai saukar Angulu 412, Tsigumi UAV da Alpha Jet daga kasar Amurka."

"Budu da kari, gwamnatin tarayya ta saki kudade somin sayan sabbin jirage Tucano daga gwamnatin kasar Amurka, yayinda ake sauraron wasu sabbin jirage masu saukar angulu 5 daga kasar Itlaiya"

Ya kara da cewa duk da jita-jitan cewa yan ta'adda sun shigo Najeriya daga kasar Syria da Iraqi, dakarun sojin Najeriya na samun nasarori kan yan ta'adda a yankin Arewa maso gabas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel