Zabe: Dabarun 'yan siyasar Najeriya 5 na jan ra'ayin masu jefa kuri’a

Zabe: Dabarun 'yan siyasar Najeriya 5 na jan ra'ayin masu jefa kuri’a

Guguwar zabe na ci gaba da bugowa, inda yan siyasa ke ta hada-hadar ganin sun samu goyon bayan jama’a.

Da kuri’un talakawa ne kadai yan siyasar za su samu damar hayewa kujerun mulki da suke muradi.

A ranar 16 ga watan Fabrairu ne dai za a fara zabe a kasar inda za a fara da masu neman kujerar Shugaban kasa da yan majalisar dokokin kasar.

Daga bisani na gwamnoni da na majalisun jiha zai biyo baya a watan Maris.

Zabe: Dabarun 'yan siyasar Najeriya 5 na jan ra'ayin masu jefa kuri’a

Zabe: Dabarun 'yan siyasar Najeriya 5 na jan ra'ayin masu jefa kuri’a
Source: Depositphotos

Akwai 'yan takarar shugaban kasa saba'in da uku, wadanda suka hada da Shugaba mai ci Muhammadu Buhari na jam'iyya mai mulki APC da mai kalubalantarsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar adawa ta PDP.

Ga wasu daga cikin hanyoyin da yan siyasa kan bi wajen siye zukatan al’umma:

1. Kyaututtukan jan ra'ayi:

'Yan siyasa da dama a Najeriya kan samar da kyaututtukan jan ra'ayi kamar huluna da riguna da litattafan rubutu da mayafai da tabarau da sauransu.

Irin wadannan kyayyaki sukan kasance dauke da hotunan 'yan takara, da tambarin jam'iyya, tare da wasu rubutattun bayanai.

2. Halartar tarurrukan al'umma:

An sha sukar lamirin 'yan siyasar Najeriya kan nesanta kansu da talakawan karkararsu, wasu ma har shafe watanni ko shekaru suke yi ba tare da sun ziyarci al'ummarsu ba, amma ba sa yin sakacin (kai ziyarar) da zarar a shiga hada-hadar yakin neman zabe.

Lamari ne da aka saba da shi a ga 'yan siyasa suna halartar tarukan al'umma ba kakkautawa - ko da ba a gayyace su ba lokacin da zabe ya karato.

Cikin sauki za a gan su suna mu'amala da talakawa a wajen bukukuwan aure da tarukan addini da sauransu. A lokuta da dama, sukan bayar da gudunmuwa, har ma su bayyana ra'ayinsu na siyasa.

3. Zayyanar kawata ababen hawa:

Wata dabarar 'yan siyasar Najeriya ta jan ra'ayin masu yin zabe, ita ce yin zayyanar kawata ababen hawa da hotuna da tambarin jam'iyyarsu.

Wadannan ababen hawa akan bai wa magoya baya su yi ta hawa suna kewaya gari da zuwa tarukan yakin neman zabe. Wadannan zane-zanen fenti bambarakwai a ababen hawa sukan dauki hankalin mutane, tare da tuna wa masu kada kuri'a cewa wane (ko su wane) na takara.

4. Raba kudi:

Siyasar kudi na daya daga jiga-jigan al'adun da ke da tasiri a siyasar Najeriya.

Wasu 'yan siyasa ko 'yan korensu a kan gan su a garuruwa da kauyuka suna watsa kudi inda ake raba kan talakawa da su.

A wasu lokutan a kan hango 'yan siyasar sun daga wa mutane hannu daga cikin motocinsu ta saman rufi ko ta taga, suna watsa kudi, yayin da masu yin zabe ke jinjina musu, tare da turereniyar karbar kudi.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Rabon kudin Kamfen ya tada kura tsakanin Ummi Zeezee da wasu manyan yan wasa

5. Alkawuran siyasa:

'Yan siyasar Najeriya kan yi dabarar alkawuran siyasa (wadanda ba su da tabbas), inda masu takarar mukaman siyasa kamar na shugaban kasa da gwamnonin jihohi kan yi alkawuran da ba su da tabbas.

Wato za su bayar da mukaman siyasa ga 'yan wata kabila ko wani yanki matukar aka goya musu baya suka samu kuri'un da suka kai su ga gacin lashe zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Shafin Naij.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel