Mahaifiya ta ce ta bani umarnin sanya wa Mahaifi na guba cikin abinci - Dan shekara 10 ya yi fallasa a gaban Kotu

Mahaifiya ta ce ta bani umarnin sanya wa Mahaifi na guba cikin abinci - Dan shekara 10 ya yi fallasa a gaban Kotu

A yayin da Hausawa kan ce 'dan Kuka da bai ji ba kuma bai gani ba ya ke janyowa Uwar sa duka, hakan kuwa ta kasance ga wata Mata da 'dan da ta haifa ya yi ma ta zundur ta hanyar yaye ma ta zani a gaban Kotu wajen tona makircin da ta aikata.

Mahaifiya ta ce ta bani umarnin sanya wa Mahaifi na guba cikin abinci - Dan shekara 10 ya yi fallasa a gaban Kotu

Mahaifiya ta ce ta bani umarnin sanya wa Mahaifi na guba cikin abinci - Dan shekara 10 ya yi fallasa a gaban Kotu
Source: Twitter

Mun samu cewa, a yau Litinin, wani Yaro mai shekaru goma a duniya ya shaidawa wata Kotun al'adu da ke zaman ta a birnin Ibadan yadda Mahaifiyar sa ta umarce shi akan sanya Guba cikin ruwan wanka da kuma abincin Mahaifin sa.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Mahaifiyar yaron, Adenike Ayodele, ta shigar da korafi a gaban kotun na neman salwantar da auren ta da maigidan ta, Adeshina, bayan sun shafe tsawon shekaru 15 da ta misalta su a zama na kunci da kuma kaddara.

Sakamakon soyayyar da ke tsakanin wannan Uba da dan sa, Yaron yayin zayyana shaidar sa a gaban kotu, ya labarta yadda mahaifiyar sa ta rika ba shi wani gari tare da umartar sa akan yaryadawa cikin abinci da kuma ruwan wanka na Mahaifin sa.

KARANTA KUMA: Rarrashi ya cancanci Matan da suka zubar da ciki ba hukunta su ba - Fafaroma

Cikin na sa martanin, Adeshina ya yi na'am da neman raba auren da ke tsakanin sa da Matar sa. Sai dai ya musanta tuhumar keta haddi da zargin cin zarafin Matarsa kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito.

Bisa ga kudira da kuma iko na Alkalin kotun, mai shari'a Ademola Odunade, ya daga sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu tare da umartar Adenike da ta gabatar da Mahaifa ko kuma waliyyan ta domin su zamto shaida yayin zartar da hukunci daidai da bukatar ta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel