Rarrashi ya cancanci Matan da suka zubar da ciki ba hukunta su ba - Fafaroma

Rarrashi ya cancanci Matan da suka zubar da ciki ba hukunta su ba - Fafaroma

- Fafaroma ya yi kira kan jin kan Mata da suka afka cikin ibtila'in zubar da ciki

- Fafaroma ya ce Matan da suka zubar da ciki sun cancanci rarrashi da jajantawa

- Ya ce akwai mummunan bala'i na bakin ciki da Mata ke fuskanta yayin yanke shawarar rabuwa da jaririn da ke ciki gabanin su haife shi.

A yau Litinin, jagoran mabiya addinin Kirista 'yan akidar Katolika na duniya, Jorge Mario Bergoglio, da aka fi sani da Fafaroma, yayi karin haske kan hukuncin jin kai da ya cancanci Matan da suka zubar da jiki a madadin hukunta su.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Fafaroma ya misalta zubar da jiki a matsayin wani babban ibtila'i da yake afkawa Mata da a cewar sa sun cancanci jin kai na rarrashi da kuma jajanta ma su.

Da ya ke ganawa da manema labarai bayan dawowar sa daga ziyarar kwanaki shida da ya kai kasar Panama, Fafaroma ya ce zubar da ciki wani bigire ne na sharadin tuba da ya cancanci a jajantawa Mata tare da rarrashi a madadin hukunta su.

Rarrashi ya cancanci Matan da suka zubar da ciki ba hukunta su ba - Fafaroma
Rarrashi ya cancanci Matan da suka zubar da ciki ba hukunta su ba - Fafaroma
Asali: Depositphotos

Ya ke cewa, akwai babban tashin hankali da mafi munin bakin ciki da Iyaye Mata ke fuskanta a yayin yanke shawarar rabuwa da jaririn da ke cikin su gabanin su haife shi.

Yayin ziyarar da ya kai kasar Panama, Fafaroma cikin hudubar sa ya yi kira kan haramcin misalta zubar da ciki a matsayin zalunci tare da neman watsi da dokokin hukunta Matan da suka zubar da ciki a duk fadin duniya.

KARANTA KUMA: Sunayen kungiyoyi 116 na Najeriya, 28 na kasa da kasa da za su sanya idanun lura a zaben 2019 - INEC

Rahotanni sun bayyana cewa, Fafaroma na yanzu ya sha bamban da sauran magabatan sa ta fuskar rashin tsauri na ra'yi da zafi na akida, inda ya ke ci gaba da kiraye-kirayen rangwanta wa wadanda suka kaucewa tafarki madaidaici.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, Fafaroma yayin jaddada yadda Mai Kowa mai Komai ya tsarkaka da Rahama, ya ce Matan da suka zubar da ciki tuni sun shiga rumfa ta yalwar gafara da jin kai na Madaukaki.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel