2019: Isa Yuguda ya bayyana dalilin sa na goyon bayan Shugaba Buhari

2019: Isa Yuguda ya bayyana dalilin sa na goyon bayan Shugaba Buhari

Mun samu labari daga jaridar Daily Trust ba da dadewa ba cewa tsohon gwamna Malam Isa Yuguda na jihar Bauchi, yayi alkawarin cewa za su ba shugaban kasa Muhammadu Buhari tarin kuri’u a 2019.

2019: Isa Yuguda ya bayyana dalilin sa na goyon bayan Shugaba Buhari
Tsohon Gwamna Yuguda yana tare da Shugaba Buhari yanzu
Asali: Depositphotos

Jaridar ta rahoto tsohon gwamnan yana alkawarin cewa wata kungiyar sa mai suna Miners for Buhari/Osinbajo (M4BO), za ta kawowa shugaban kasa Buhari da Osinbajo akalla kuri’a miliyan 5 a zaben shugaban kasa da za ayi.

Isa Yuguda yace kokarin da gwamnatin Buhari tayi wajen tada harkar ma’danai ya sa wannan kungiya ta su za ta goyi bayan ‘dan takaran shugaban kasan na APC. Yuguda yayi mulki ne a jihar Bauchi daga 2007 inda ya zarce zuwa 2015.

KU KARANTA: 2019: Jam'iyyar adawa ta AA tayi wa Shugaba Buhari mubaya’a

Malam Isa Yuguda yace a gwamnatin APC, masu hakar ma’adanai akalla mutum miliyan 5 su ka samu abin yi, don haka yace za su sakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari ta hanyar kada masa kuri'a domin ya zarce a zaben 2019.

Wanda ya tara ‘yan wannan kungiyar ta masu hako ma’adanai, Alhaji Saleh Katsina, ya bayyana cewa kudin shigan da aka samu ta harkar hako albarkatun kasa a Najeriya ya karu yanzu daga Biliyan 2 zuwa Biliyan kusan Biliyan 4.

Idan ba ku manta ba Isa Yugudu ya lashe zaben 2007 ne a karkashin jam’iyyar ANPP, amma daga baya ya sauya-sheka zuwa PDP mai mulki a wancan lokaci. Bayan saukar sa gwamna, Yuguda ya koma GPN amma daga baya ya tsere.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel