Makircin yahudawa: An bukaci musulmai su kauracewa sayen takardar kewaye mai dauke da sunan Allah

Makircin yahudawa: An bukaci musulmai su kauracewa sayen takardar kewaye mai dauke da sunan Allah

An bukaci daukacin al'ummar musulmai da su kauracewa wata takardar goge najasa kamar su kashi ta M&S sakamakon wani rubutu dake ishara da sunan Allah dake a saman ta da larabci kamar dai yadda wasu 'yan uwa suka bankado.

Labarin takardar dai yayi ta yaduwa ne kamar wutar daji a kafafen sadarwar zamani kamar su dandalin Youtube, Facebook da dai sauransu biyo bayan wani bidiyo da wani bawan Allah yayi yana ankarar da jama'a.

Makircin yahudawa: An bukaci musulmai su kauracewa sayen takardar kewaye mai dauke da sunan Allah

Makircin yahudawa: An bukaci musulmai su kauracewa sayen takardar kewaye mai dauke da sunan Allah
Source: UGC

KU KARANTA: Sabon bincike ya bankado wasu sirrikan Walter Onnoghen

Legit.ng Hausa ta samu cewa mutane da dama dai sun yi ta bayyana ra'ayoyin su game da lamarin inda wasu ke ganin kamfanin yana sane yayi hakan domin tozarci da kuma takalar fada yayin da wasu kuma ke ganin ba haka bane.

Al'umma da dama dai na ganin koma dai meye musabbabin yin hakan, ya kamata musulmai a dukkan fadin duniya su rika taka-tsantsan wajen siyen ababen tu'ammalin su na yau da kullum.

Haka zalika dai mai karatu zai iya tuna cewa ba wannan ne karon farko fa da yahudawa da turawan yamma ke shirya irin makircin nan ga al'ummar musulmai amma kuma a ko yaushe sukan gano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel