Latest
A lokacin da yake shirye-shiryen kama aiki a karo na biyu, a ranar 22 ga watan Mayu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci ministoci da su mika shugabanci ga sakatarorin din-din-din na ma’aikatunsu daban-daban.
Kamar yadda muka sani hijabi wani tufafe ne da mata ke amfani dashi wajen yane kansu da jikinsu. Hijabi kan karawa mace kima da zati a cikin al’umman Musulmi kasancewar Allah ne ya umurci mata da su sanya hijabi.
A yau Asabar, 8 ga watan Yuni ne, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Sani Abacha ya cika shekaru 21 da mutuwa. An haifi Janar Sani Abacha ranar 20 ga watan Satumbar shekarar 1943 a cikin garin Kano.
Akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa rikici tsakanin gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya zo karshe biyo bayan wata matsaya da aka cimma a daren ranar Juma’a a Abuja.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an yi bikin ne a babban otal din birnin Instanbul mai suna Bosphorus, inda Ozil ya auri sahibarsa, Amine Gulse, yayin da shugaba Erdogan da matarsa Emine suka halarci bikin.
Wasu yan fashi da makami sun kai ma wani mutum hari sannan suka yi masa fashin naira miliyan 1.5 a garin Bauchi. Lamarin ya afku ne a ranar Jumaúnguwar Wunti kusa da shataletalen babba kasuwa a garin Bauchi.
Legit.ng ta ruwaito a ranar Juma’a ne EFCC ta janye daga wannan shari da aka kwashe sama da shekaru 8 ana fafatawa, inda ta mika karar zuwa ga ofishin babban lauyan gwamnati, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.
Sabon Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila Autan Bawo, ya dakatar da hakimai biyu a masarautarsa biyo bayan zargin rashin biyayya yayinda rikici ke ci gaba da kunno kai a tsarin sarauta a jihar.
A kwanan nan ne aka yi bikinwani mutumi mai suna Kabiru Mohammed Garkuwa a garin Jos inda ya auri santala-santala yan mata guda biyu a rana daya.
Masu zafi
Samu kari