Sai na tsugana sannan na ke ba Miji na abinci – Inji Jaaruma

Sai na tsugana sannan na ke ba Miji na abinci – Inji Jaaruma

Mun samu labari cewa Fitacciyar Malamar matan nan watau Hauwa Saidu Mohammed, wanda aka fi sani da Jaaruma ta fito tayi bayani game da yadda ake tafiyar da rayuwar aure har ya daure.

Jaaruma tayi wannan jawabi ne ta wani bidiyo da ta saki kwanan nan inda aka ga tana dukawa har kasa idan za ta ba Mai gidan ta abinci. Jaaruma tayi kaurin-suna wajen harkar rayuwar aure.

Wannan Baiwar Allah ta ke cewa: “Sunana Jaaruma, kuma ina girmama Miji na. Ina dukawa idan zan ba Miji na abinci.” Jaaruma ta kara da cewa: “Kyawun mace bai rike namiji a wajen diya mace.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sake kai wani mumunan hari a Jihar Katsina

Sai na tsugana sannan na ke ba Miji na abinci – Inji Jaaruma
Jaaruma ta na ba Mai gidan ta abinci har kasa a baki
Asali: Instagram

“Ladabi da biyayya daga kowane bangare ne kurum ya ke rike aure.” Jaaruma ta bayyana duk wannan ne a bidiyon da ta fitar a lokacin da ta tsuguna har kas domin ta ba Mai gidan ta abinci.

Jaaruma ta maida martani ne ga ‘Yan matan da ke ganin kyawun su zai sa Namiji ya zauna da su komai runtsi. Jaaruma ta na ganin komai munin mace idan ta iya kwanciya, za ta rike Namiji.

Jaaruma, mai shekaru kusan 26 a Duniya, asalin ta Mutumiyar Garin Billiri ce daga jihar Gombe, wanda tayi fice wajen saida kayan mata da kuma bada shawarwarin yadda za a rike Mijin aure.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel