'Yan ta'adda sun sake kai hari jihar Katsina

'Yan ta'adda sun sake kai hari jihar Katsina

A yayin da ake ci gaba da fuskantar kalubale na nau'ikan ta'addanci daban daban babu dare babu rana musamman a Arewacin Najeriya, mun samu cewa 'yan ta'adda sun sake kai wani mummunan hari jihar Katsina.

Harin da ya auku da sanyin safiyar ranar Asabar da ta gabata a kauyen Zaka na karamar hukumar Safana, ya salwantar da rayukan 'yan uwan juna uku da suka fito daga ciki daya kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

An gabatar da gawawwakin wadanda suka riga mu gidan gaskiya a fadar sarkin Katsina, Mai Martaba Abdulmumin Kabir, bayan an garzaya da su da Yammacin Asabar tare da Mahaifiyar su cikin zubar hawaye.

Dogaran fadar Katsina sun shawarci 'yan uwan wadanda suka riga mu gidan gaskiya da su koma da gawawwakin zuwa mahaifar su domin gudanar da jana'iza tare da shimfide su a gidan su na karshe.

Kakakin masarautar Katsina, Mallam Iro Bindawa, ya shawarci dagacin kauyen Zaka da ya bayyana wa fadar Katsina a rubuce dukkanin yadda ta kasance yayin aukuwar wannan mummunar annoba.

KARANTA KUMA: Mutane 4 da za su yi sulhu a tsakanin Sarki Sanusi da Ganduje

SP Gambo Isah, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari yayin bayar da shaidar cewa harin ya auku yayin da 'yan ta'adda suka kai farmaki kan 'yan uwan junan uku a wata gonar su dake bayan gari.

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan, wani matashi, Musa Isuhu da ya shahara a kan zartar da ta'addanci cikin jihohin Zamfara da kuma Katsina ya shiga hannun jami'an tsaro inda ya amsa laifin salwantar da rayukan mutane da dama a karo daban daban.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel