Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa Suntai, matar da tsohon gwamnan jihar Taraba, Marigayi Danbaba Suntai, ya mutu ya bari ta auri Haliru Saad Malami, matashin dan kasuwa dake rike da mukamin babban mai zartar wa na kamfanin ITBAN Global Resources LTD.

Haliru, wanda aka fi sani da San Turakin Malumfashi, dan asalin jihar Katsina ne.

Hauwa, haifaffiyar 'yar Musulmai daga jihar Borno, ta auri tsohon gwamna Suntai, duk da kasancewarsa Kirista, a wasu shekaru da dama da suka shude.

Emmanuel Bello, hadimin marigayi Suntai, ya karyata rahotannin da suka bayyana cewar Hauwa ta koma addinin Musulunci. A cewar sa, Hauwa ba ta taba fita daga addinin Musulunci ba.

DUBA WANANNA: Gwamnatin tarayya ta canja salon tafiyar tuhumar da EFCC ke yi wa Goje

Jaridar Daily Nigerian ta ce Malami, angon Hauwa, dan uwa ne ga Turai Yar'adua, matar tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa Yar'adua.

Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa da San Turakin Malumfashi

Hauwa, matar tsohon gwamnan arewa da ya mutu ta auri San Turakin Malumfashi

Hauwa ta auri San Turakin Malumfashi
Source: Twitter

Suntai, tsohon mijin Hauwa, ya mutu ne a ranar 28 ga watan Yuni na shekarar 2017 a garin Houston na kasar Amurka bayan ya sha fama da rashin lafiya sakamakon hatsarin jirgin saman da ya yi a watan Oktoba na shekarar 2012.

Malami, mai shekaru fiye da 30, ya auri Hauwa, mai shekaru fiye da 50, ranar Asabar. Ba a wani gayyaci jama'a masu yawa ba a wurin daurin auren da aka yi a babban Masallacin birnin tarayya, Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel