An dakatar da Hakimai 2 saboda rashin biyayya ga masarautar Rano

An dakatar da Hakimai 2 saboda rashin biyayya ga masarautar Rano

Sabon Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila Autan Bawo, ya dakatar da hakimai biyu a masarautarsa biyo bayan zargin rashin biyayya yayinda rikici ke ci gaba da kunno kai a tsarin sarauta a jihar.

Hakiman da abun ya shafa sun hada da na Bebeji, Alhaji Haruna Sanusi, wanda a yan makonnin baya sa sanar da murabus dinsa daga mukaminsa don nuna goyon baya ga Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi amma daga bisani ya nesanta kansa daga wasikar bisa ga wani dalili da ba a sani ba.

An kuma tattaro cewa sarkin Rano, ya dakatar da hakimin garin Tudun Wada, Dr. Bashir Muhammad.

Hakan ya warware mukaman da hakiman biyu ke rike dashi a matsayin “Dan Galadima Kano” da “Dan Kadai Tudun Wada”.

Sakataren masarautar Rano, Alhaji Muhammad Idris Rano ne ya aike masu da sakon dakatarwar ta wasika.

A cewar sakataren masarautar, cikin wasikar dakatarwar, ma’aikatar kananan hukumomi na sane da sane da matakin.

KU KARANTA KUMA: Yadda aka yi na auri mata biyu a rana daya - Magidanci

A wani labarin kuma mun ji cewa dattaijon dan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya shawarci masu binciken zargin almundanar kudi a masarautar Kano su kasance masu gaskiya da adalci wurin gudanar da aikinsu.

A yayin da ya ke tsokaci kan takardan neman ba'asi da gwamnatin Kano ta aike wa Sarki Sanusi a ranar Alhamis, dattijon ya ce takardan neman ba'asin ba abin tayar da hankali bane ila wata hanya ce na gano gaskiya a cikin kowanne lamari.

Ya shawarci Sarkin ya yi nazarin dukkan zargin da ake masa ya kuma bayar da amsoshi inda ya ce abinda ya da ce shine idan ana zargin mutum da aikata wani abu sai a bashi ikon ya mayar da ba'asi ya kuma kare kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel