EFCC ta janye karar data shigar da Goje bayan ya janye daga takarar shugabancin majalisa

EFCC ta janye karar data shigar da Goje bayan ya janye daga takarar shugabancin majalisa

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta janye daga shari’ar da take yi da tsohon gwamnan jahar Gombe, Sanata Danjuma Goje, awanni kadan bayan ya janye daga takarar kujerar shugaban majalisar dattawa.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Juma’a ne EFCC ta janye daga wannan shari da aka kwashe sama da shekaru 8 ana fafatawa, inda ta mika karar zuwa ga ofishin babban lauyan gwamnati, kuma ministan shari’a, Abubakar Malami.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun dandana kudarsu a hannun Sojojin Najeriya a Adamawa

EFCC ta janye karar data shigar da Goje bayan ya janye daga takarar shugabancin majalisa

Danjuma Goje
Source: Facebook

Sai dai masu bibiyan al’amuran siyasar Najeriya sun danganta wannan mataki da hukumar ta dauka ga sulhun da shugaban kasa yayi tsakanin masu neman kujerar shugabancin majalisar dattawa a jam’iyyar APC, Sanata Ahmad Lawan da Danjuma Goje.

Sai dai yayin da Lawan keda goyon bayan shugaban kasa da uwar jam’iyyar APC, Goje a hannu guda shi kadai yake yakinsa, kuma da alama yana da damar da zai bata ma Lawan rawa, don haka gwamnan jahar Kaduna, Nasir El-Rufai ya ja shi zuwa fadar shugaban kasa domin Buhari ya lallasheshi.

Bayan wannan zama da aka yi a ofishin shugaban kasa a ranar Alhamis ne sai kwatsam Goje ya sanar da janyewarsa daga takarar kujerar shugabancin majalisar, tare da jaddada goyon bayansa ga Sanata Ahmad Lawan, a ranar Juma’a kuma EFCC ta sakan masa mara, kowa dai ya san ruwa baya tsami banza.

A yayin zaman kotun na yau da aka kira cikin gaggawa, lauyan EFCC Wahab Shittu ya bayyana ma Alkalin dake sauraron karar, Babatunde Quadiri cewwa hukumar ta janye daga cikin wannan sharia, kuma ta mikashi zuwa ga ofishin ministan sharia.

Shima a nasa jawabin, lauyan Danjuma Goje, Paul Erokoro bai nuna tirjiya game da matakin da hukumar EFCC ta dauka ba, yayin da Alkalin lauyan gwamnati daya bayyana a zaman, Pius Asika ya shaida ma kotun cewa ya dauki ragamar cigaba da shari’ar, amma a daga zaman zuwa wani lokaci na daban.

Bayan sauraron dukkanin bangarori uku ne sai Alkalin kotun ya sanar da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel