Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, an Kashe Manyan Kwamandojin Boko Haram a Borno

Sojoji Sun Yi Ruwan Wuta kan 'Yan Ta'adda, an Kashe Manyan Kwamandojin Boko Haram a Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun kwashi kashinsu a hannu bayan da dakarun sojojin sama suka kai hare-hare a maboyarsu a Borno
  • Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama tare da lalata kayayyakin aikinsu bayan kai hari da daddare
  • Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka wasu kwamandojin kungiyar Boko Haram yayin harin da suka kai a yankin Bulabulin

​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun sojojin sama na rundunar Operation Hadin Kai sun gudanar da wani harin sama na dare a maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Bulabulin a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun samu nasarar karkashe ’yan tada ƙayar baya da dama, ciki har da manyan kwamandoji biyu.

Sojoji sun kashe kwamandojin Boko Haram a Borno
Dakarun sojojin Najeriya a bakin daga Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun hallaka jagororin 'yan ta'adda a Zamfara bayan yi masu ruwan wuta

Sojoji sun farmaki 'yan ta'adda

Majiyoyi sun bayyana cewa an kai harin ne a sa’o’in farko na ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026 biyo bayan ingantattun bayanan sirri da aka samu kan motsi da taruwar ’yan ta’adda a cikin yankin.

Sun kuma bayyana cewa harin ya farmaki wasu muhimman wurare na ’yan ta’adda da kuma kayayyakin aikinsu a cikin maɓoyar.

A cewar majiyar, an lalata motoci da gine-gine da dama na ’yan ta’adda yayin luguden wutar, yayin da aka kashe ’yan tada ƙayar baya da dama a aikin.

“Harin saman ya yi nasara. Tantance barnar da aka yi bayan fafatawar da kuma sanya ido na bayanan sirri sun tabbatar da cewa an karkashe ’yan ta’adda da dama yayin harin."

- Wata majiya

An kashe manyan kwamandojin Boko Haram

Majiyar ta ƙara bayyana cewa manyan kwamandojin ƙungiyar Boko Haram guda biyu da ke gudanar da ayyuka a yankin Bulabulin suna cikin waɗanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna a Katsina, an kashe tsageru

“An tantance su a matsayin Karma Wakil, wanda shi ne kwamandan da ke kula da yankin Bulabulin, da kuma mataimakinsa, Wali Matari."

- Wata majiya

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji na ci gaba da farmakar 'yan ta'adda

A cewar majiyar sojoji, wannan aikin wani ɓangare ne na ci gaba da kai hare-hare da dakarun sama na Operation Hadi KaI ke yi don raunana shugabancin ’yan ta’adda, lalata hanyoyin samar musu da kayan aiki, da kuma hana ’yan tada ƙayar baya damar yin zirga-zirga a faɗin yankin Arewa maso Gabas.

Majiyar ta ce ana ci gaba da gudanar da ayyukan sanya ido bayan harin domin tabbatar da irin girman asarar da aka yi wa ’yan ta’addan.

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin Najeriya sun fafata da 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Rundunar sojojin ta bayyana cewa an kashe sojoji biyu yayin da suke fatattakar wani hari da mayakan 'yan ta’adda na ISWAP suka kai a wani sansanin da ke Magumeri.

A cewar sanarwar da aka fitar, dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda da dama yayin artabun da aka yi

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng