Shahararren dan kwallon Arsenal ya yi aure, shugaban kasa ya halarta
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mesut Ozil ya angwance a ranar Juma’a a babban birnin kasar Turkiyya, Instanbul, inda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya samu halartar.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an yi bikin ne a babban otal din birnin Instanbul mai suna Bosphorus, inda Ozil ya auri sahibarsa, Amine Gulse, yayin da shugaba Erdogan da matarsa Emine suka halarci bikin.
KU KARANTA: Mutane 3 sun halaka a sanadiyyar tashin bom a jahar Imo
Tun a shekarar 2017 Ozil ya fara soyayya da buduwarsa, Amine, wanda hakan ya nuna shekaru biyu kacal suka kwashe suna soyayya kafin suka yi aure, haka zalika a shekarar data gabata ne Ozil ya nemi shugaba Erdogan ya zama babban abokin angonsa.
A ranar Alhamis, 6 ga watan Yuni ne Ozil ya yi kira ga masoyansa masu bukatar bashi kyautukan biki dasu taimaka ma gidauniyarsa a wani muhimmin aiki da take yin a taimaka ma kananan yara marasa lafiya masu bukatar aikin tiyata a asibiti.
“Nida Amine zamu dauki nauyin yima kananan yara 1000 aikin tiyata, don haka duk mai niyyar bamu kyauta a wannan bikin ya aika kudinsa zuwa ga www.bigshoe.info/donate.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng