Masarautar Katsina ta nada sabbin masu zaben sarki

Masarautar Katsina ta nada sabbin masu zaben sarki

Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, Sarkin Katsina ya nada Galadiman Katsina da Durbin Katsina a matsayin masu zaban sarki a masarautar.

Masarautar da Katsina ta nada Justice Sadiq Abdullahi Mahuta (murabus) ne a matsayin Galadiman Katsina (na 11) kuma Hakimin Malumfashi bayan rasuwar marigayi Justice Mamman Nasir.

Sarautar Galadima tana daya daga cikin manyan sarautu a masarautar kasancewar sa daya daga cikin masu zaben sabon sarki. Sauran masu zaben sarkin sune Kauran Katsina, Yandakan Katsina da Durbin Katsina.

DUBA WANNAN: Daga karshe: Sarki Sanusi ya bayar da kan amsa tuhumar da Ganduje ke masa

Fadar sarkin Katsina ta cika makil da 'yan uwa da abokan arziki da masu taya murna da suka hallarci taron.

Nadin sarautar ya ci karo da nadin wasu masu zaben sarkin, Durbin Katsina kuma Hakimin Mani, Alhaji Umar Babani da kuma Hakimin Kafur kuma Dan Galadiman Katsina, Alhaji Rabe Abdullahi.

Wasu da aka yi wa nadin sarautar sun hada da Magajin Radda, Kabir Umar, Magajin Garin Danmusa, Sani Muaazu, Magajin Iyatawa, Hassan Junaidu da Magajin Gobir, Tanimu Kabir.

Manyan mutanen da suka hallarci taron sun hada da gwamnan Katsina, Aminu Masari, mataimakinsa, Mannir Yakubu, tsohon gwamnan Katsina, Abba Musa Rimi, tsaffin mataimakan gwamna biyu, Tukur Jikamshi da Abdullahi Garba Faskari.

Sarki Abdulmumin Kabir Usman da ya jagoranci nadin sarautan Galadiman Katsina ya bukaci ya yi aiki tuquru domin kare hakkin talakawa da darajar masarautar.

Ya yi addu'ar Allah ya kawo sauki kan kallubalen tsaro da ake fama da shi a jihar inda ya ce harkar tsaro nauyi ne da ya rataya a kan kowa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel