Zaben 2019: Ku bamu shahadarmu, zababbun yan majalisa 5 na Bauchi sun fada wa INEC

Zaben 2019: Ku bamu shahadarmu, zababbun yan majalisa 5 na Bauchi sun fada wa INEC

- Alhaji Garba Dahiru tare da sauran yan majalisa hudu da hukunci kotu ya shafa na ganin nawar hukumar zabe mai zaman kanta wurin ba su shahadarsu

- Garba wanda shi ne sanata mai wakiltar Bauchi ta kudu ya yi wannan jawabin ne yayin wata zantawa da manema labarai wacce ta samu halartar sauran yan majalisun hudu

Zababbun ‘yan majalisar dokokin tarayya su biyar daga jihar Bauchi, wadanda kotu ta bai wa hukumar zabe mai zaman kanta umarni ta mika masu shahadarsu sun fara korafi a kan batun.

Yan majalisar dai sun hada da sanata daya tare da ‘yan majalisar wakilai mutum hudu. Da yake tsokaci a kan wannan batu, Alhaji Garba Dahiru (PDP) wanda shi ne zababben sanata mai wakiltar Bauchi ta kudu ya ce: “ Tun a ranar 16 ga watan Mayun 2019 Jastis Bello Kawu ya bada wannan umarnin.”

KU KARANTA:Kaakakin majalisa: An nemi Dogara ya koma karo na 2

A cewarsa: “ Kotu ta bada umarnin cewa INEC ta mika shahada ga duk dan takarar da ya zo na biyu a yankin Bauchi ta kudu da kuma sauran gundumomin majalisar wakilai ta tarayya a zaben da ya gabata."

Yan majalisa hudun da ke jiran shahadar kamar yadda hukuncin kotu ya shata su ne; Abdulkadir Ibrahim (Alkaleri/Kirfi, PDP), Dayyabu Chiroma (Darazo/Ganjuwa, PRP), Awwal Jatau (Zaki, PDP) da Isa Muhammad Wabu (gundumar Gamawa, NNPP).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: